Lokacin samun kudi a banza ya wuce – Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa lokacin samun kudi a banza ya wuce inda ya ce babu sauran kudin da za a rika diba ana watsarwa.Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana haka ne a Gusau fadar Jihar Zamfara, a shekaranjiya Laraba lokacin da yake bude hanyar Wanke zuwa danjibga zuwa Kuchire zuwa Kigama zuwa Bilbis.Shugaba […]
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa lokacin samun kudi a banza ya wuce inda ya ce babu sauran kudin da za a rika diba ana watsarwa.
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana haka ne a Gusau fadar Jihar Zamfara, a shekaranjiya Laraba lokacin da yake bude hanyar Wanke zuwa danjibga zuwa Kuchire zuwa Kigama zuwa Bilbis.
Shugaba Buhari wanda ya bukaci ’yan Najeriya su rika tunani kan halin da kasar nan take ciki ya ce: “Lokacin samun kudi a banza ya wuce kuma babu kudin da za a rika watsarwa a kasa. Wajibi ne mu koma ga noma da kiwo ta yadda za mu iya bunkasa masana’antu, wajibi ne mu zage dantse wajen tabbatar da cimma burinmu na sake gina Najeriya.”
Shugaban kasar ya nanata kudirin gwmnatinsa na cewa ba za ta sassauta kan yaki da cin hanci da rashawa da take yi a yanzu ba, inda ya ce, cin hanci da rashawa da almundahana ne suka hana kasar ci gaba.
Ya ce, gwamnatinsa ba ta da niyyar musgunawa ko cin zarafin wani mutum, kuma ya yi alkawarin kudaden da aka kwato daga barayin gwamnati za a sanya su inda za su amfani jama’a.
“Kuma ina so in nanata wa jama’ar Jihar Zamfara da na Najeriya baki daya cewa kudirin wannan gwamnati na tsabtace harkokin mulki da na gwamnati na nan. Za mu ci gaba da aiwatar da yaki da cin hanci da rashawa da almundahana. Ba mu da buri ko sha’awar tozartawa ko cin mutuncin wani mutum, amma wajibi ne mu kwato kudin gwamnati da aka sace, mu yi wa jama’a aiki,” inji shi.
Buhari ya ce, tunda aka rantsar da gwamnatinsa a ranar 29 ga Mayun bara, aka fara aiwatar da shirin gyaran kasar nan. Ya ce kalubalen da gwamnatinsa ke fuskantar shi ne yadda za ta kawo canjin da ake bukata a aikace, inda ya ce hakan ba zai samu ba, sai an samu dabi’ar rikon amana da kyakkyawan shugabanci. “Ina tabbatar wa ’yan Najeriya cewa kuncin tattalin arziki da dukkan jama’a ke ciki abu ne mai gushewa,” inji shi.
Ya ce, harkokin tsaro na inganta, inda hobbasar gwamnatinsa na tabbatar da tsaro yana haifar da da mai ido. Kuma ya je Zamfara da kansa ne don kaddamar da yaki da barayin shanu da ’yan fashi domin ganin bayan wannan danyen aiki ba a Jihar Zamfara kadai ba har ma da daukacin jihohin Arewa maso Yamma.