Yadda Jiragen Sojin Najeriya Suka kashe Fararen Hula 400 Bisa Kuskure

Jiragen sojin Najeriya sun kashe farare hula sama da 400 daga 2014, a bisa kuskure.

Yadda Jiragen Sojin Najeriya Suka kashe Fararen Hula 400 Bisa Kuskure

Fararen hula sama da 400 jiragen sojin Najeriya suka kashe a bisa kuskure a kasar daga shekarar 2014 zuwa yanzu.

Harin da wani jirgi mara matuki ya kai wa masu taron Mauludi a Jihar Kaduna ranar Lahadi shi ne na 16 kuma mafi muni, inda aka rasa kimanin mutun 90.

Na biye da shi, shi ne wanda aka rasa rayuka 60 a Zamfara, sai na uku wanda aka rasa wasu 58 a Borno.

Sau shida irin haka na faruwa a Jihar Borno.

Ga jerin lokutan da irin haka ta faru da kuma yawan fararen hula da aka yi asara:

  1. Mutum 10 a Jihar Borno a harin ranar 16 ga watan Maris, 2014.
  2. Mutum 58 a Borno 17 ga watan Janairun 2017
  3. Mutum 20 a 28 ga watan Fabrairun 2018
  4. Mutum 11 a Zamfara ranar 11 ga Afrilun 2019
  5.  Mutum 13 a ranar 2 ga Yulin 2019
  6. Mutum 30 a Borno ranar 25 ga Afrilun 2021.
  7. Mutum 9 a Yobe a ranar 26 ga watan Satumbar 2021
  8. Mutum 20 a Borno a ranar 26 ga watan Satumbar 2021.
  9. Mutum 6 a Neja a ranar 20 ga watan Afrilun 2022.
  10. Mutum 12 a Katsina a ranar 6 ga watan Yulin 2022.
  11. Mutum 60 a Zamfara a ranar 17 ga watan Disambar 2022.
  12. Mutum 18 a Neja a ranar 24 ga watan Janairu 2023.
  13. Mutum 40 a Nassarawa ranar 25 ga Janairu
  14.  Mutum 3 a Kaduna a ranar 5 ga watan Maris sin 2023
  15. Mutum 1 a Neja a ranar 18 ga Agustan 2023.
  16. Mutum 90+ a Kaduna a ranar 3 ga Dismabar 2023.