Lookman ya lashe kambun gwarzon dan kwallon Afirka na 2024

A lokacin karbar kyautar, Lookman ya gode wa ‘yan wasan tawagarsa, masu horaswa da iyalinsa, wajen taimaka masa.

Lookman ya lashe kambun gwarzon dan kwallon Afirka na 2024

Ademola Lookman ya lashe kambun gwarzon dan kwallon Afirka na 2024, inda ya doke ‘yan wasa kamar su Adingra, Guirassy, Hakimi, da Inaki Williams.

Jajircewar Lookman a kungiyar Atalanta a gasar Serie A, da rawar da ya taka wajen taimaka wa kungiyar da kuma gudummawar da ya bai wa tawagar Najeriya, suka sa ya zama wanda ya fi kowa cancanta wajen lashe wannan kyauta.

Lookman ya bayyana jin dadinsa na lashe kyautar ta wannan shekarar, kuma masoyansa sun bayyana jin dadinsu yadda ya ci kwallaye da kuma taimaka wa kungiyarsa.

A lokacin karbar kyautar, Lookman ya gode wa ‘yan wasan tawagarsa, masu horaswa, da iyalinsa, wajen taimaka masa.

“Wannan kyauta ta cika min burina, kuma ina fatan hakan zai zaburar da matasa daga Afirka su yarda da kansu.

“Wannan nasara tana nuna aikin tukuru da sadaukarwa da na yi.”

Wannan nasara ta kara tabbatar da matsayin Lookman a matsayin daya daga cikin taurarin Afirka masu haskawa.

Magoya baya daga fadin nahiyar Afirka sun yi murna da wannan nasara, inda Lookman ya shiga cikin jerin manyan ‘yan wasan Afirka da suka lashe wannan kyauta.

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu