Lubabatu I. Garba, a Kano Ranar Talatar da ta gabata, 17 ga watan Nuwamba ta zama ranar da ’yan fim xin Hausa ba za su tava mantawa da ita ba, kasancewar ta zama ranar da suka rasa uwa kuma kaka a gare su, wato Mama Mai Aya, kamar yadda suka fi kiranta.

Ranar Talatar da ta gabata, 17 ga watan Nuwamba ta zama ranar da ’yan fim din Hausa ba za su taba mantawa da ita ba, kasancewar ta zama ranar da suka rasa uwa kuma kaka a gare su, wato Mama Mai Aya, kamar yadda suka fi kiranta.Hajiya Hafsatu Muhamamd Sharada, wacce aka fi sani da […]

Lubabatu I. Garba, a Kano Ranar Talatar da ta gabata, 17 ga watan Nuwamba ta zama ranar da ’yan fim xin Hausa ba za su tava mantawa da ita ba, kasancewar ta zama ranar da suka rasa uwa kuma kaka a gare su, wato Mama Mai Aya, kamar yadda suka fi kiranta.
Lubabatu I. Garba, a Kano Ranar Talatar da ta gabata, 17 ga watan Nuwamba ta zama ranar da ’yan fim xin Hausa ba za su tava mantawa da ita ba, kasancewar ta zama ranar da suka rasa uwa kuma kaka a gare su, wato Mama Mai Aya, kamar yadda suka fi kiranta.

Ranar Talatar da ta gabata, 17 ga watan Nuwamba ta zama ranar da ’yan fim din Hausa ba za su taba mantawa da ita ba, kasancewar ta zama ranar da suka rasa uwa kuma kaka a gare su, wato Mama Mai Aya, kamar yadda suka fi kiranta.
Hajiya Hafsatu Muhamamd Sharada, wacce aka fi sani da Mai Aya, ta rasu a gidanta da ke unguwar Sharada, sakamakon fama da rashin lafiyar da ta yi. ta rasu ta bar ’yaya biyu, namiji da mace.
An dauki tsawon lokaci Mama Mai aya na fama da ciwon sukari, inda lokaci-kokaci yakan tayar mata. Sai dai a wanann lokacin ciwon ya kama ta da karfi, inda ta shafe tsawon watanni bakwai a kwance tana faman jinya.
Hajiya Rukayya Muhamamd, ’ya ce ga Mama Mai Aya. Ta bayyana cewa mahaifiyar tata ta yi fama da ciwon kafa, inda har ta kai ba ta iya yin komai da kanta. “Kin san tana da ciwon sukari, to wannan karon ciwon kafa ne ya matsanta mata har ta kasance ba ta iya tashi har zuwa ranar da Allah Ya karbi abarSa.”
Ta bayyana mahaifiyarta da cewa: “Mahaifiyarmu ta kula da mu sosai, ta tarbiyyantar da mu yadda ya kamata. Babu abin da za mu ce sai dai mu yi mata fatan samun rahamar Allah.”
Binciken Aminiya ya gano cewa marigayiyar ta fara harkar wasan kwaikwayo ne a shekarar 1980, a gidan talabijin na Muhahamdu Abubakar Rimi, a lokacin ana kiransa da sunan CTb, inda suke wasan kwaikwayo mai suna Zaman Duniya. Daga baya kuma ta shiga harkar fina-finan Hausa, inda har ta yi Fina-finai masu yawan gaske.
Aminiya ta gano cewa marigayiyar ta fara wasan kwaiwkayo na fina-finan Hausa tun wajen shekarar 1995, inda ta yi fina-finai irinsu Tantiri da Zarge da sauransu. Sai dai fim din da ya zamo wa marigayiyar na karshe shi ne fim din Hajiya Babba.
Malam Bashir Nayaya, wanda aka fi sani da dan Magori yana cikin mutanen da suka yi hulda da marigayiya a matsayin abokan sana’ar juna tun daga kan wasan kwaikwayon talabijin har zuwan na fina-finan Hausa. Ya bayyana marigayiyar da cewa mace ce mai hakuri da fara’a. “Mace ce mai fara’a da son zumunci. Da zarar ta ga an dauki kwanaki ba ku hadu ba, to za ta neme ka don ta ji lafiyarka. Haka kuma idan wani abu ya samu mutum na dadi ko akasinsa, tana kan gaba wajen taya mutum murna ko jaje. Haka kuma mace ce mai kazar-kazar, wacce ba ta wasa da aikinta,” inji shi.
Hajiya Hajara Usman tana daga cikin wadanda suke harkar sana’ar fim din Hausa da marigayiya Mai Aya. Ta bayyana marigayiyar da cewa a matsayin uwa mai daukar kowa a matsayin ’ya’yanta. “Ni Hajiya uwa ce a wurina, domin tana dauka ta a matsayin ’yarta. Koyaushe muka hadu da ita, za ka ji ta fara yi min addu’a tare da sa min albarka. Hakan ba karamin dadi yake yi min ba. Shi ya sa lokaci-lokaci nakan ziyarce ta, inda ita kuma za ta yi ta yi min addu’a,” inji ta.
Ta shaida wa Aminiya cewa haduwarsu ta karshe da marigayiyar shi ne kimanin makonni biyu da suka gabata, a lokacin da ta je duba jikinta. “Kasancewar na san tana kwance ba lafiya, lokaci-lokaci nakan je gidanta na duba ta. Mun yi haduwar karshe makonni biyu da suka gabata, inda har take gaya min irin yadda take fama da jiki. Da zan tafi ta yi ta yi min addu’a tana cewa Allah Ya shi min albarka. Ashe ban sani ba karshen ganin ke nan.”
Shi ma wani wanda suka taba aikin wasan kwaikwayo a talabijin tare da marigayiyar, Malam Yakubu Ibrahim, ya bayyana ta a matsayin mace wacce ta iya hulda da jama’a da kuma daukar sana’arta da mahimmanci. “Mun yi aiki tare da marigayiya Hajiya Hafsatu shekaru masu yawa, a lokacin muna wasan kwaikwayon gidan talabijin. Babu shakka mace ce da ta iya hulda da jama’a kowa kuma nata ne. Haka kuma duk da cewa a wancan lokaci ba kudi ake ba mu ba, da muke wasan gidan talabijin amma matar nan ba ta wasa da aiki. Idan aka sa lokaci, to a kan lokaicin za a ganta. Mace ce mai hakuri da barkwanci. Muna yi mata addu’a Allah Ya jikanta, Ya kuma yi mata rahama.”
Aminiya ta tattauna da dan wasa, furodusa sannan kuma darakta Iliyasu Abdulmumni Tantiri, wanda ya bayyana marigayiyar a matsayin mace mai barkwanci da kuma son jama’a. “Babu shaka ita mutumwa aba ce mai ciwo, musamman mutuwar wanda ka shaku da shi. Rasuwar Marigayiya Mama Mai Aya rasuwa ce da ba iyalinta kadai aka yi wa ba, rashi ne ga dukkanin ’yan masana’antar Kannywood; kasancewar dai dai ne a cikinmu masu sana’ar da zai ce bai yi hulda da wannan baiwar Allah a cikin wannan masana’anta ba. Na san marigayiya tun wajen shekarar 1995, inda har muka yi fim din Tantiri. Mama Mai Aya mace ce mai hakuri da son jama’a, ga ta da barkwanci. Haka kuma mace ce mai son aiki. Idan aiki ya hada ku ba ta wasa sai ta ga ta sauke nauyin da ke kanta,” inji Tantiri.
Shi ma Shugaban kungiyar Masu Sana’ar Fim ta Arewa (AFMAN), Malam Jamilu Ahmed Yakasai ya bayyana cewa kungiyarsu tana cikin alhini na rashin uwa kuma kaka a masana’antar fim gaba daya “kungiyar Arewa tana cikin alhinin rashin Mama Mai Aya, macen da ta kasance uwa kuma kaka a wanann masana’anta tamu. Mace ce da ta sadaukar da lokutanta wajen ciyar da wannan masana’anta gaba. Mama Mai Aya ita ke bin masana’antarmu bashi. Sai dai mu biya ta da addu’a, Allah Ya yi mata rahama, Ya yafe mata kura-kuranta. Mama ta tafi a lokacin da muke bukatarta, kasancewar a kullum muna karuwa daga abubuwan da tsofaffin cikinmu ke gaya mana.”
Daga cikin wadanda suka halarci jana’izarta sun hada da Bashir Nayaya da Alhaji Leko da Sogiji da Malam Haruna Sarauniya da Kabiru Maikaba da suaransu. Shi ma Shugaban Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano, Malam Isma’ila Na’abba Afakallah yana daga cikin wadanda aka yi jana’izar marigayiyar tare da su.