Lubabatu I. Garba da Saddam Mohammed, Kano
Hankula sun fara kwantawa a garin Saminaka da ke karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna bayan da aka samu tashin hankali a Unguwar Abadawa da ke kusa da garin a ranar Litinin da ta gabata. Rikici wanda ya yi sanadin asarar rayukan mutum hudu tare da raunata mutane da dama ya taso ne sakamakon murnar […]
Hankula sun fara kwantawa a garin Saminaka da ke karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna bayan da aka samu tashin hankali a Unguwar Abadawa da ke kusa da garin a ranar Litinin da ta gabata.
Rikici wanda ya yi sanadin asarar rayukan mutum hudu tare da raunata mutane da dama ya taso ne sakamakon murnar cin zaben da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata.
Wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa rikicin ya fara tashi ne da misalin karfe 2:00 na rana, bayan da wasu matasa suka shiga Unguwar Abadawa suna murnar nasarar zabe, inda suka samu matsala da matasan unguwar inda rikici ya barke a tsakaninsu.
Wannan rikici ya kai ga sanya shingaye da farfasa wuraren kasuwanci da kone babura a ranar.
Rikicin ya kwanta bayan da sojoji da ’yan sanda suka zo suka kora mutane zuwa gidajensu. Sai dai ricikin ya sake tashi a unguwar a washegari da safe inda aka sake
sanya shingaye, al’amari da ya tayar hankulan al’ummar garin Saminaka inda al’amura suka tsaya.
Wannan ne ya sanya aka kafa dokar hana fita a garin Saminaka da kewaye, sannan aka turo karin ’yan sandan kwantar da tarzoma da sojoji daga Kafanchan.
A zantawarsa da wakilinmu Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, DSP Zubairu Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce wasu mutane ne suke murnar cin zaben da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata suka je wata unguwa da ake kira Abadawa a kusa da garin Saminaka, sai suka samu matsala da matasan unguwar abin ya zama kamar fada, inda aka ji wa mutane rauni, kuma Sarkin unguwar ya sanar da jami’an tsaro aka zo aka kwantar da rikici.
Ya ce ya zuwa wannan lokaci ba su samu labarin asarar rai ba, amma sun kama mutum biyu suna ci gaba da bincike a kan lamarin.
Ya ce sun tura ’yan sanda kuma hankula sun fara kwantawa a yankin.
Shugaban riko na karamar Hukumar Lere Alhaji Ibrahim Abdulkarim Lazuru ya nuna takaicinsa kan faruwar lamarin. Ya ce, “A gaskiya ba mu ji dadin faruwar wannan
lamari ba. Amma mun gode Allah domin a yanzu komai ya lafa sakamakon daukar matakan tsaro da aka yi.”
Ya ce, babu shakka babban jami’in ’yan sandan yankin ya yi iyakar kokarinsa tare da ’yan sandansa, kuma Kwamnadan ’Yan sandan Shiyyar Kafanchan ya kawo motoci 12 na sojoji da ’yan sanda don kwantar da rikicin. Sai ya yi kira ga al’ummar karamar hukumar sun kwantar da hankalinsu su ci gaba da harkokinsu cikin zaman lafiya.