Lucky Aiyedatiwa ya lashe zaɓen Gwamnan Ondo

Aiyedatiwa, ya samu nasara da ƙuri’u 366,781, inda ya doke babban abokin hamayyarsa, Ajayi Agboola na jam’iyyar PDP, wanda ya samu ƙuri’u 117,845 kacal. 

Lucky Aiyedatiwa ya lashe zaɓen Gwamnan Ondo

Bayan shafe watanni ana yaƙin neman zaɓe, al’ummar Jihar Ondo, sun zaɓi Lucky Aiyedatiwa na jam’iyyar APC a matsayin gwamnan jihar, wanda zai mulke su na tsawon shekaru huɗu masu zuwa.

Babban jami’in tattara sakamakon zaɓen jihar, Farfesa Olayemi Akinwumi, wanda shi ne Mataimakin Shugaban Jami’ar Tarayya ta Lokoja, a Jihar Kogi, ya ayyana Aiyedatiwa a matsayin wanda ya yi nasara a ranar Lahadi.

Ya ayyana sakamakon ne, a cibiyar tattara sakamakon zaɓe ta INEC da ke Akure.

Aiyedatiwa, ya samu nasara da ƙuri’u 366,781, inda ya doke babban abokin hamayyarsa, Ajayi Agboola na jam’iyyar PDP, wanda ya samu ƙuri’u 117,845 kacal.

Wannan ya bai wa ɗan takarar APC tazarar ƙuri’u sama da 200,000.

“Ɗan takarar APC, Lucky Orimisan Aiyedatiwa, wanda ya cika dukkanin sharuɗan doka, an ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara,” in ji Akinwumi.

Jam’iyyar APC ta lashe dukkannin ƙananan hukumomin jihar 18, lamarin da ya tabbatar da nasarar Aiyedatiwa.

Nasarar ta ba shi damar yin tazarce a mulkinsa, bayan zaɓarsa a matsayin gwamna a watan Disamban 2023, bayan rasuwar gwamna Rotimi Akeredolu.

Aiyedatiwa, wanda ya taɓa zama mataimakin gwamnan jihar, ya karɓi ragamar mulki bayan Akeredolu ya ba shi ragamar mulki lokacin da yake fama da rashin lafiya.

Bayan rasuwar Akeredolu, Aiyedatiwa ya samu tikitin takarar gwamna na jam’iyyar APC don shiga zaɓen 2024.

Ya fafata da sauran ‘yan takara 17, ciki har da Agboola, wanda shi ma ya taɓa riƙe muƙamin mataimakin gwamna a wa’adin farko na Akeredolu.

A lokacin yaƙin neman zaɓensa, Aiyedatiwa ya yi alƙawarin bunƙasa tattalin arziƙi da walwalar ma’aikatan jihar.

Ya kuma amince da ƙarin mafi ƙarancin albashi na Naira 73,000, wanda ya ninka na Gwamnatin Tarayya na Naira 70,000.

Lucky Aiyedatiwa ya lashe zaɓen Gwamnan Ondo

Ba na yi wa Tinubu hassada — Atiku

Kama matashiya kan sukar Gwamnan Sakkwato ya tayar da ƙura

Babban Limamin Minna Sheikh Isa Fari ya rasu