Luis Suárez zai bar Atletico Madrid a karshen kakar wasanni
Dan wasan ya fara tunanin neman sabuwar kungiya da zai ci gaba da murza leda.
Atletico Madrid ta sanar da cewar dan wasan gabanta Luis Suárez zai bar kungiyar da zarar an kammala kakar wasanni ta bana.
Suárez ya shafe shekara biyu a kungiyar, bayan barin kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, inda ya lashe gasar Laliga a bara.
- Zan dama da ’yan Kudancin Kaduna a mulkina —Sani Sha’aban
- Kullum kara kaunar Adam A. Zango nake yi —Safiya Chalawa
Atletico Madrid ta tabbatar da cewar ba za ra sabunta kwantaraginsa dan wasan mai shekara 35 a duniya.
Tuni wakilin dan wasan dan asalin kasar Uruguay ya soma laluben nema masa sabuwar kungiya amma a nahiyar turai.
Luis Suárez ya buga wa Atletico Madrid wasanni 44 a bana, inda ya zura kwallo 13 a raga.
Dan wasan ya bar Barcelona a 2020 bayan da sabon kocinta a lokacin, Ronald Koeman ya ce ba ya daga cikin ‘yan wasan da zai yi amfani da su.