Lulu Briggs: Yadda rikici ya hana binne biloniya bayan shekara da rasuwarsa
A ranar 27 ga Disamban nan ne hamshakin attajiri kuma basarke Cif O.B Lulu-Briggszai cika shekara daya da rasuwa, amma rikci a tsakanin iyalansa ya hana a dauko gawarsa daga Accara babban birnin kasar Ghana zuwa mahaifarsa a jihar Ribas balle a yi maganar binne shi. Lulu-Briggs wanda ya yi fice wajen taimakon jama’a shi ne […]
A ranar 27 ga Disamban nan ne hamshakin attajiri kuma basarke Cif O.B Lulu-Briggszai cika shekara daya da rasuwa, amma rikci a tsakanin iyalansa ya hana a dauko gawarsa daga Accara babban birnin kasar Ghana zuwa mahaifarsa a jihar Ribas balle a yi maganar binne shi. Lulu-Briggs wanda ya yi fice wajen taimakon jama’a shi ne mai Kamfanin Mai fetur na Monu Polo Oil, kuma ya rasu ne ranar 27 ga Disamba bara a Ghana, amma rikici a tsakanin iyalansa kan abin da ya yi ajalinsa ya hana binne shi. Dansa na biyu Cif Duno Briggs ya gayyaci ’yan sanda kan su binciki musabbabin rasuwar mahaifin nasu, wanda hakan na daya daga cikin dalilan da suka dabaibaye rufe mamacin.
Matar mamacin, Dokta Seinye Lulu Briggs a cikin wata wasika da ta fitar a watan Yulin bana wadda ta rubuta wa iyalan mamacin ta bukaci su mayar da wukakensu cikin kube su bari a yi wa mijinta sutura.
A cikin wasikar ta ce “A matsayina na matar marigayi Lulu Briggs kuma uwar ’ya’yansa ina rokon da ku mayar da wukakenku cikin kube lura da cewa Opuda ya rasu tun ranar 27 ga Disamban bara.”
Don haka ta nemi su hada kawunansu su tunkari yadda za a yi shirye-shiryen bikin binne shi yadda ya kamata.
Rigimar ta cikin gida ta faro ne lokacin da dangin mamacin a karkashin jagorancin Oruwari Briggs suka fitar da wata sanarwa a watan Mayn bana, inda suka yi kururuwar neman sanin inda dan uwansu kuma shugaban Oruwari Briggs yake.
A cikin sanarwar wacce Cif A.B Ajumogobia da Cif Ibim Masi Briggs da Cif Solomon W.Y Briggs da wadansu mutum hudu suka sa wa hannu, dangin Lulu Briggs sun shelanta cewa ba su san inda dansu yake ba, wanda a cewarsu iyalansa sun fada musu cewa wai ya rasu a ranar 27 ga Disamba bara a kan hanyarsa ta zuwa kasar Ghana. Sun shelanta cewa tunda aka ce ya tafi Ghana ba su kara jin duriyarsa ba. Sun ce in ya rasu ne suna bukatar ganin gawarsa tare da takardar da ke nuna shaidar inda ya rasu da yadda ya rasu.
Dan mamacin na biyu Duno Briggs yana musayar yawu da matar mahaifinsa a kan wanda zai karbi gawar. Duk da yake Duno yana zargin kishiyar mahaifiyarsa da jan kafa wajen ganin an binne mamacin, a waje daya kuma sanarwar ta ce dukkansu suna fada ne a kan dukiyar da marigayin ya bari.
Manyan mutane ciki har da tsofaffin Shugabannin Kasa, Cif Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan sun yi kokarin shiga tsakani don daidaita iyalan marigayin a samu a binne shi, amma har zuwa yanzu lamarin ya ci tura.
Ana cikin wannan tataburzar ce kuma Gwamnatin Jihar Ribas ta yi wa iyalan mamacin tayin daukar nauyin bikin binne shugaban na Kalabari. Da yake bada wannan sanarwa a Larabar makon jiya a Gidan Gwamnati, Gwamnan Jihar Ribas, Cif Nyesom Wike ya ce gwamnatinsa tana son daukar nauyin yi wa marigayin biso ta ban girma.
“Na fada musu su bar Gwamnatin Ribas ta dauki nauyin binne shi. Abin da kawai nake son gani shi ne a samu zama lafiya a tsakanin iyalansa,” inji Wike.
Ya ci gaba da cewa “Ta yaya za a ce mutum kamar wannan shugaba na Kalabari kuma babba a kasa, ya rasu kimanin shekara daya amma a ce har yau ba a binne shi ba?
“Na yi kokarin shiga tsakani har sau uku amma matarsa tana ba ni ciwon kai. Ya kamata su bari a rufe shi tukuna daga nan duk wani mai korafi a kan dukiyar da ya bari sai ya je gaban hukuma,” inji Gwamnan.