Lura da fuska ta hanyar turarawa
Kowace mace tana da burin samun fuska mai kyawu, mai sheki ba tare da kuraje ko tabo ba. Tabbas fitowar kuraje a fuska na daya daga cikin matsalolin da ke bata kwalliyar mace. Wadansu kurajen duk hodar da aka sanya wa fuska ba za su bata ba. Hodar ba za ta iya boye kurajen ba […]
Kowace mace tana da burin samun fuska mai kyawu, mai sheki ba tare da kuraje ko tabo ba. Tabbas fitowar kuraje a fuska na daya daga cikin matsalolin da ke bata kwalliyar mace. Wadansu kurajen duk hodar da aka sanya wa fuska ba za su bata ba. Hodar ba za ta iya boye kurajen ba saboda girmansu. Wannan dalilin ya sa muka kawo muku yadda za ku lura da fuskarku ta hanyar turarawa.
Da farko, ku samu ruwan dumi, sannan ku turara fuskarku. Hakan na magance fitowar kuraje, idan kuma sun fito zai magance su. Turara fuska na bude kofofin fata, musamman ma wadanda gumi ko datti suka toshe su. Idan gumi da datti suka toshe kofofin fata sai maiko ya taru a fuska, a karshe ya haifar da kurajen fuska. Don haka za ku samu zuma mai kyawu, sai ku hada ta da ruwa, sai ku rika sha da safe kullum, yin hakan zai haifar muku da fata mai laushi da kuma sheki.
Turara fuska na taimaka wa jinin jikinmu zagaya fuska ba tare da daukar lokaci ba, saboda turaren ya tsabtace fuska, ya kuma bude kofofin fatar fuska. Za ku iya turara fuska a gida, ba wai sai kun je asibiti ko wani wuri ba.
Yadda ake turara fuska
Ku zuba ganyen tyme da ruwan lemon tsami a cikin ruwa, daga nan ku tafasa shi. Idan ruwan ya tafasa sai ku sauke shi. Daga nan ku rufe kanku da tawul domin turirin ruwan ya turara fuskarku, amma a dan yi baya da robar ruwan zafin domin kada ku kone. Turara fuska sau daya a sati na hana fitowar kuraje.