Luwaɗi: An yanke wa ɗalibai biyu hukuncin bulala a bainar jama’a

Za a zartar da hukuncin yi wa ɗaliban biyu bulala gabani ko bayan watan Azumin Ramadana.

Luwaɗi: An yanke wa ɗalibai biyu hukuncin bulala a bainar jama’a

Wata kotu a lardin Aceh da ke ƙasar Indonesia ta yanke wa wasu ɗalibai maza biyu hukuncin bulala a bainar jama’a.

A ranar Litinin ce kotun ta yanke wa mutanen biyu hukuncin bayan samun su da laifin luwaɗi da juna.

A yayin da mu’amala tsakanin jinsi ɗaya ta halasta a wasu yankunan ƙasar mafi rinjayen musulmi a duniya, sai dai ɗabi’ar ta haramta a lardin Aceh da aka ayyana dokokin shari’ar Musulunci.

Tun a watan Nuwamban bara ne dai ’yan sanda masu ɗabbaka shari’a suka kama mazajen biyu da ke karatu a wata jami’a suna aikata wannan alfasha a wani ɗaki da suka kama haya a birnin Banda Aceh.

Jami’i mai shigar da ƙara mai suna Alfian ya ce Kotun Shari’a ta Banda Aceh ta samu mutanen biyu da laifin luwaɗi kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP ya ruwaito.

Kotun ta yanke wa ɗaya daga cikinsu bulala 85 saboda shi ne ja gaba wajen kama hayar ɗakin yayin da ta yanke wa ɗayan hukuncin bulala 80 a cewar Alfian.

Alfian ya ce za a zartar da hukuncin yi wa ɗaliban biyu bulala gabani ko bayan watan Azumin Ramadana.

Zartar da hukuncin bulala a bainar jama’a ba sabon lamari ba ne a lardin Aceh kan laifukan da suka haɗa da caca, shan barasa ko zina.

Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil Adama na adawa da hukuncin bulala a bainar jama’a da suke ɗauka a matsayin zalunci, sai dai wannan doka karɓaɓɓiya ce a wurin mazauna lardin Aceh.

A shekarar 2021 ce aka yi wa wasu ma’aurata masu auren jinsi bulala.

Haka kuma, a watan Janairun da ya gabata ne aka yi wa wasu maza huɗu bulala saboda caca a yanar gizo, hukuncin da shi ne na farko da aka zartar bana.