Luwadi da yara 4 ya kai malami gidan yari a Kaduna

Malamin yana yaudarar samarin zuwa dakinsa inda yake yin lalata da su

Luwadi da yara 4 ya kai malami gidan yari a Kaduna
Wata Kotun Majistare da ke Kafanchan a Jihar Kaduna ta tasa keyar wani malamin makaranta mai suna Josiah Alkali zuwa gidan yari bisa zargin sa da yin lalata da wasu yara maza hudu.

Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya (NSCDC) ce ta gurfanar da malamin mai shekaru 40 kan yin lalata da wasu yara maza hudu masu shekaru 13 zuwa 15 a dakinsa.

Jami’i mai shigar da kara na NSCDC, Marcus Audu, ya shaida wa kotun cewa malamin ya lalata da yaran ne a lokuta da dama daga watan Fabrairu zuwa Yulin 2024.

Ya ce wanda ake tuhumar ya rika yaudarar kowanne daga cikin yaran ne a lokuta daban-daban zuwa dakinsa da ke Takau inda ya yi lalata da su ta dubura.

A cewarsa, wanda ake tuhuma ya yi barazanar kashe yaran idan suka gaya wa wani abin da ya yi musu.

Mai gabatar da kara ci gaba da cewa a yayin gudanar da bincike, wanda ake tuhumar ya amsa laifinsa

Alkalin kotun, Samson Kwasu, ya yi watsi da ikirarin wanda ake kara na rashin hurumin kotun na sauraren karar.

Kwasu ya umurci mai gabatar da kara da ya mika kwafin fayilolin karar zuwa ofishin kararrakin jama’a na Jiha domin samun shawara.

Bayan haka, ya dage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 25 ga watan Yuli.