Luwadi: Magijanci ya lalata dan shekara 5 a Zariya

Yaron ya ce mutumin ya yi masa fyade akalla sau uku kafin dubunsa ta cika a yanzu

Luwadi: Magijanci ya lalata dan shekara 5 a Zariya

Mutanen unguwa sun kama wani magidanci mai shekara 45 kan zargin sa da lalata wani yaro ɗan makarantar firamare ta hanyar luwadi a yankin Zariya ta Jihar Kaduna.

Al’ummar yankin sun ce dama ana zargin mutumin da yi wa yara maza fyade, don haka suke ta bibiyar motsinsa, kuma yaron ya faɗa da bakinsa cewa kusan sau uku mutmin yana ɗaukar sa.

Wanda ke zargin yana sana’ar sayar da rake ne a Bakin Dago Tudun Jukun a Karamar Hukumar Zariya Jihar Kaduna.

Aminiya ta ziyarci xibiyar da ke kula da cin zarafin mata da ƙananan yara da ke Asibitin Gambo Sawaba Kofar Gayan Zariya domin samun sahihin bayani kan lamarin a likitance.

Manajar Cibiyar, Hajiya A’isha Ahmed ta ce a ranar 12 ga watan 2 2025 ofishin ’yan sanda da ke Gonar Ganye, gundumar Tukur Tukur ya kawo wani yaro ɗan shekara 5 kuma ɗan aji ɗaya a makarantar firamare da ake zargin mutumin da lalatawa.

Bayan likitoci sun duba sun gano cewa yaron duburarsa ta bude, wanda hakan ke nuni da an yi yunƙurin zakke masa ta duburarsa.

Hajiya A’isha Ahmed ta ce sun dora yaron a kan magani har na tsawon kwanaki 28 kuma za su rika bibiyar sa domin su tabbatar da cewa yana amfani da maganin yadda ya kamata.

Ta ci gaba da cewa za ta tura sakamakon zuwa ga Kwamishinan Lafiya na Jihar Kaduna, kuma ta tabbatar da cewa sun bai wa jami’an ’yan  sanda kwafin binciken.

Hajiya A’isha Ahmed ta yi kira ga iyaye da su daina boye irin wannan mugun abin da ke faruwa da yaransu wai don gudun abin kunya ko halin da yaran za su shiga.

Ta kara da cewa zuwa asibitin da yaran da aka ci zarafinsu a kan lokaci yana taimakawa wajen kula da lafiyarsu.

Mahaifin yaron da aka ɓata ya koka kan yadda ya ce wasu makusantan wanda ake zargin suke ƙoƙarin ɗanne shi da kuma kare shi wanda ake zargin.

Ya ce “abin mamaki shi ne ta yadda suka bi ta hannun mai anguwa wai a bani kuɗi na bar maganar,” DOn haka ya ce a shirye yake da ya bi haƙƙin ɗan nasa domin daƙile irin hakan a nan gaba ga ’ya’yan wasu.

Duk ƙoƙarin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, ASP Mansur Hassan, ya ci tura, domin layin wayarsa ta ƙi shiga, kuma har rubutaccen sakon da aka aika masa bai amsa ba.