Ma su cewa Buhari ya sauka ba su san ciwon kansu ba – Imam Usama

Aminiya; A makon da ya gabata ne wasu suka yi zanga-zanga da kiraye-kirayen cewa shugaban kasa Muhammad Buhari ya dawo daga jinyar da ya tafi waje, ko kuma ya sauka. Ya ya ka kalli wannan al’amari?  Usama; Gaskiyar magana wadannan mutane da suke zanga-zanga ko kuma kiraye-kirayen cewa shugaban kasa Muhammad Buhari ya sauka, a […]

Ma su cewa Buhari ya sauka ba su san ciwon kansu ba – Imam Usama

Aminiya; A makon da ya gabata ne wasu suka yi zanga-zanga da kiraye-kirayen cewa shugaban kasa Muhammad Buhari ya dawo daga jinyar da ya tafi waje, ko kuma ya sauka. Ya ya ka kalli wannan al’amari?

 Usama; Gaskiyar magana wadannan mutane da suke zanga-zanga ko kuma kiraye-kirayen cewa shugaban kasa Muhammad Buhari ya sauka, a tsaya ana sauraronsu ma bata lokaci ne, domin ba su sun san ciwon kansu ba. Saboda idan muka duba a zamanin gwamnatin da ta gabata a kullum  ana kashe daruruwan mutane ana kone garuruwa da kauyuka a kasar nan. Amma duk da wadannan miyagun abubuwa da suka rika faruwa a lokacin babu wanda ya fito ya ce Shugaban kasa na lokacin Goodluck Jonathan ya sauka. Hatta a lokacin da ya yi niyyar zarcewa, babu wanda ya iya fitowa ya yi magana kai, haka aka ba shi dama ya yi takara aka kayar da shi.

 Amma saboda rashin tunanin sai shugaban kasa Muhammad Buhari wanda aka sami cigaba a kasar nan sakamakon zaben da aka yi masa a matsayin shugaban kasa. Domin ya sami nasara kashi 85 bisa 100 a bangaren tsaro a kasar nan. Haka kuma ya sami nasara kan yaki da cin cin hanci da rashawa. Kuma a lokacin zai tafi sai da ya baiwa mataimakinsa rikon shugabancin kasar nan. A tarihin mulkin damokuradiyya a Najeriya, ba a taba samun shugaban kasar da ya yi haka ba. Ya rubutawa majalisa kuma ta bashi izini. Domin shi mutum ne mai bin doka da oda.

 Al’ummar Najeriya sun fahimci cewa shugaban Buhari yana kokarin kawo gyara a Najeriya. Kuma sun fahimci cewa shi ba barawo ba ne. Don haka Najeriya basu damu ba, kan wannan al’amari suke cigaba da ba shi goyon baya da hadin kai. Masu adawa da wannan gwamnati ne da ake bincike ne suke turo irin wadannan masu zanga-zanga da kiraye-kirayen ya sauka. Kuma irin wadannan masu adawa sune suka kirkiri yunwa da talauci a kasar nan, domin su bata wannan gwamnati.

 Aminiya; Mane ne ra’ayinka dangane da masu neman a sake tsarin fasalin kasar nan?

 Usama; Wane fasali ake son a sakewa kasar nan? Wane irin gyaran kundin tsarin mulkin ne ba ayi ba a kasar nan? Ai gyara fasalin kasar nan shi ne abi dokokin kasar. Wato ya zama kowa ya bi dokokin kasa ba tare da nuna cewa wasu sun fi karfin doka ba. Ya kamata duk wanda ya karya doka a hukunta shi. Amma in ya zama akwai wasu shafaffu da mai, wadanda suka fi karfin doka za a cigaba da samun matsala a kasar nan. Idan har a baya za a iya hukunta Obasanjo ko Shehu Musa ‘Yardauwa ko Abiola a kasar nan, ka ga ya nuna cewa a baya babu wanda ya fi karfin hukunci a kasar nan.

 Amma yanzu a kasar nan akwai mutanen da suka fi karfin hukunci. Yanzu a kasar nan duk laifin da ka yi idan ka dauki lauya ka je kotu, shike nan maganar ta mutu. Yanzu shari’a ta zama kamar wani abin sayarwa a Nijeriya. Idan ka yi laifi ka kawo kudi sai a sayar maka. Don haka abin da ya kamata a gyara ke nan a Nijeriya, wato abi dokokin Nijeriya ba tare da nuna bambanci ba.

 Aminiya; Yaya kake kallon harin da ‘yan Boko Haram suka kai a kwanakin baya, a wajen da ake aikin hakar mai a yan yankin tafkin Chadi dake jihar Barno, wanda aka kashe mutane da dama?

 Usama; Wannan yanki na Maiduguri akwai arziki iri daban-daban kuma manyan munafukan duniya sun san da wannan arziki na yankin Maiduguri. Don haka irin wadannan abubuwa da suke faruwa a wannan yanki, akwai abin da ake son a cimma. Kuma maganar da mutanen kudu suke yi cewa ‘yan arewa ba su da komai, cima zaune ne, suna fadin haka ne don suna ganin suna da mai. To yanzu Allah Yasa an gano mai a wannan yanki an fara aikin hakarsa. Don haka ake ganin cewa idan aka bari aka fara hako wannan mai, abin da suke son su cimma ba zai yiwu ba.

 Don haka wannan hari wani makirci ne aka shirya don hana wannan aiki na hako mai a wannan yanki. Kuma ita wannan kungiya ta Boko Haram wata kungiya ce da wasu suke amfani da ita, wajen neman kudi. Idan har ana son a magance wannan matsala dole ne sai an binciki wadanda suke daukar nauyinsu. Domin ana zargin mutane da dama cewa suna taimaka masu. Kuma ganin irin makudan kudaden da gwamnati take kashewa a wannan yaki, wadansu da dama ba zasu so ace wannan yaki ya zo karshe ba, domin suna amfana da wadannan makudan kudade da ake kashewa.

 Amma idan a yau aka yi doka kan cewa duk wanda aka kama da laifi kan wannan al’amari komai girmansa za a hukumta shi nan take za a magance wannan matsala. Idan ka lura tun da ake wannan yaki ana ta kama mutane, amma ba a taba sa ‘yan boko haram da ka kama sun bayyana wadanda suke daukar nauyin su ba.

 Aminiya; Har yanzu masu fafutukar neman kasar Biyafara, suna nan akan bakarsu, ya ya kake kallon wannan al’amari?

 Usama; Idan ka dubi tarihin kasar nan ‘yan kudunci ne suka fara cin amanar ‘yan Arewa domin akwai yaran kudu da su Sardauna da Tafawa Balewa ne suka sanya su a makaranta, a gidajensu babu inda ba sa shiga, amma sune suka kashe su. Kuma daga baya suka zo suka ce a ba su kasar su, kuma tun daga wancan lokacin har ya zuwa wannan lokaci da muke ciki. A kullum suna zaginmu suna zagin addininmu. Shi yasa wasu ‘yan Arewa suke ganin a baiwa ‘yan Biyafara kasarsu kowa ya kama gabansa.

 Amma ni ina ganin ai a lokacin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan sun sami damar raba kasar nan, amma ba su yi haka ba. Don haka wannan fafutuka tasu karya ce, ba kasar suke son a raba ba. Idan sun ce a raba kasar nan kowa ya kama gabansa a raba, domin mun san cewa Allah ne yake azirta kowa, don haka mu a nan Arewa, Allah Zai bamu arzikin da bamu yi zata ba. Yanzu ba ga shi ana ta gano mai a Arewa ba, baya ga noma da muke yi wanda yanzu duk duniya hankali ya koma gare shi.