Ma’aikacin Bankin Sky Bank ya gurfana a gaban kotu
Wani ma’aikacin bankin Sky Bank da ke Hadeja a Jihar Jigawa mai suna Yahya Garba ya gurfana a gaban Babbar Kotun Majistare ta daya da ke Dutse bisa tuhumarsa da satar kudin masu ajiya a bankin. Bankin ne ya kai Yahya Garba gaban ’yan sanda bisa zargin yana amfani da kasancewarsa mai biyan abokan hulda […]
Wani ma’aikacin bankin Sky Bank da ke Hadeja a Jihar Jigawa mai suna Yahya Garba ya gurfana a gaban Babbar Kotun Majistare ta daya da ke Dutse bisa tuhumarsa da satar kudin masu ajiya a bankin. Bankin ne ya kai Yahya Garba gaban ’yan sanda bisa zargin yana amfani da kasancewarsa mai biyan abokan hulda da bankin ya tura kudin jama’a har Naira miliyan daya da dubu 700 cikin asusunsa. A lokacin da Alkalin Kotun Mai shari’a Mustapha Datti ya waiwayi wanda ake tuhumar, ya musanta zargin da ake yi masa, kuma lauyansa Muhammed Zakiyyu ya roki kotu ta ba da belinsa, kafin ’yan sanda su kammala bincikensu kan zargin tare da dage sauraron karar zuwa 2 ga Satumba mai zuwa. Sai dai lauyan bankin na Sky Bank, Yahaya Umar ya roki kotun ta kammala bincike a kan wanda ake tuhumar kafin ba da belinsa. Kotun ta ba da belinsa bisa sharadin mai karbar belin ya kasance ma’aikacin da ke matakin albashi na 15 kuma yana da gida a Dutse fadar jihar, tare da bayar da hotunansa biyu da takardar mallakar gidan da kuma ajiye Naira dubu 200. Mai shari’a Datti ya dage sauraron karar zuwa 2 ga Satumba mai zuwa.