Ma’aikacin Gidan Gwamnatin Borno ya rataye kansa
Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta tabbatar da mutuwar wani mai dafa abinci (Kuku) a gidan gwamnatin jihar, bayan ya rataye kansa. A ranar Talatar da ta wuce ne aka same shi matacce a saman bishiya ya rataye kansa, bayan ya kammala aikinsa na dafa abinci sannan ya raba kamar yadda ya saba. Shi dai […]
Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta tabbatar da mutuwar wani mai dafa abinci (Kuku) a gidan gwamnatin jihar, bayan ya rataye kansa.
A ranar Talatar da ta wuce ne aka same shi matacce a saman bishiya ya rataye kansa, bayan ya kammala aikinsa na dafa abinci sannan ya raba kamar yadda ya saba.
Shi dai wannan mamaci mai suna John Acagwa, wanda ya fito daga kauyen Dilai da ke yankin Karamar Hukumar Askira Uba a Jihar Borno, dan shekara 60, masu aikin kula da fulawa a wani bangare na gidan ne suka same shi rataye a saman bishiya da rana tsaka, inda suka sanar da abokan aikinsa kafin a kwanto gawarsa.
Bayanai sun tabbatar da cewar mamacin ya yi ritaya daga aiki yau kusa da shekara 10 kenan amma kuma gwamnatocin da suka wuce sun ci gaba da tafiya da shi kuma sun ba shi hakkokinsa amma wata majiya daga gidan gwamnatin ta tabbatarwa wakilinmu cewar mamacin yana bin gwamnatin Kashim shettima bashin wasu hakkokinsa kuma yana ganin ana gobe (shekaranjiya Laraba) gwamnan zai sauka daga kujerar gwamnan Jihar al’amarin da ake ganin watakila hakan ce ta sa ya rataye kansa.
Wata majihar kuma ta ce akwai daya daga cikin ’tarsa da ke bin maza, da hakan ke bata masa rai. An ce mahaifiyar yarinyar ce ke daure mata gindi da hakan ta sa yakan yawan yin korafi a duk lokacin da yake aikin dafa abinci a gidan gwamnati. “Ai na kusa bar musu duniyar” inji tsohon kamar yadda wasu na kusa da shi suka shaidawa wakilinmu ya taba fada a kwanaki.
Kwamishinan ’yan sandan Jihar Muhammad Ndatsu Aliyu ya tabbatar da aukuwar wannan al’amari. Sai dai babu wanda ya san dalilin da ya sa mamacin ya rataye kansa amma jami’ansa suna gudanar da bincike don gano musabbabin aukuwar lamarin.