Ma’aikata 774,000: Majalisa ta yi zaman gaggawa

Majalisar Dattawa ta kira taron gaggawa kan matakin ma’aikatar kwadago na ci gaba da shirin daukar ma’aikata 774,000 a Najeriya. Hakan ya faru ne bayan umarnin yin daukar ma’akatan da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba wa minista a ma’aikatar, Festus Keyamo, a ranar Talata baya majalisar ta dakatar da shirin. Da yake magana da […]

Ma’aikata 774,000: Majalisa ta yi zaman gaggawa

Majalisar Dattawa ta kira taron gaggawa kan matakin ma’aikatar kwadago na ci gaba da shirin daukar ma’aikata 774,000 a Najeriya.

Hakan ya faru ne bayan umarnin yin daukar ma’akatan da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba wa minista a ma’aikatar, Festus Keyamo, a ranar Talata baya majalisar ta dakatar da shirin.

Da yake magana da manema labarai, Keyamo ya ce Shugaba Buhari ya ba shi damar ci gaba da shirin ba tare da la’akari da matsayar Majalisar Tarayya ba a kan lamarin.

Keyamo da ‘yan majalisar sun kai ruwa rana kan zargin da ya yi musu na neman yin babakeren a shirin na daukar ma’aikatan.

Su kuma ‘yan majalisar suka zarge shi da yin gaban kansa a shirin na Hukumar Daukar Ma’aikata ta Kasa (NDE).

Hakan ya kai su ga cacar bakin da ya sa majalisar ta tsayar da shirin a makon jiya.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos