Ma’aikata ku amince da albashin Naira dubu 30 ko yin murabus- Gwamnoni
Gwamnonin Najeriya sun bukaci ‘yan kungiyar kwadago da su amince da mafi karancin albashin da aka yanke na Naira dubu 30 ko kuma su ajiye aikinsu a duk fadin kasar. An sanar da hakan ne bayan tattaunawar kungiyar Gwamnonin Najeriya suka yi jiya Laraba a Abuja. Shugaban kungiyar Gwamnoni Abdul’aziz Yari ya ce, a yanzu […]
Gwamnonin Najeriya sun bukaci ‘yan kungiyar kwadago da su amince da mafi karancin albashin da aka yanke na Naira dubu 30 ko kuma su ajiye aikinsu a duk fadin kasar.
An sanar da hakan ne bayan tattaunawar kungiyar Gwamnonin Najeriya suka yi jiya Laraba a Abuja.
Shugaban kungiyar Gwamnoni Abdul’aziz Yari ya ce, a yanzu haka sun kaddamar da kwamitin da zai gana da Shugaba Muhammadu Buhari akan bullo da hanyar magance matsalar karancin albashi.