Ma’aikatan Najeriya miliyan 71 ba za su samu karin albashi ba
Najeriya na daga cikin masu biyan albashi mafi muni a Afirka
Alkaluma na nuni da cewa daga cikin ma’aikata miliyan 76 da ke Najeriya, miliyan 5.3 ne za su amfana da karin albashin da ake shirin yi.
Hakan na zuwa ne duk da cewa bincike ya gano cewa Najeriya na daga cikin masu biyan albashi mafi muni a Afirka.
Wannan kuma na nufin duk abin da ma’aikatan da za a yi wa karin suka samu, za su raba su kai tsaye ne ko a fakaice tare da sauran ’yan kasar sama da da miliyan 224.
Alkaluman Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) sun nuna cewa ’yan Najeriya miliyan 1.5 ne ke aiki da gwamnatin tarayya.
- Wakilan Aminiya sun tsallake rijiya da baya a Kano
- NAJERIYA A YAU: ‘Kananan Hukumomi Na Daf Da Zama Mabarata’
- Mafi Ƙarancin Albashi: Muna kan buƙatarmu ta N250,000 — NLC
Wasu miliyan biyu na aiki da gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi, miliyan 1.8 kuma a kamfanoni masu zaman kansu.
A yayin da ake ci gaba da kai ruwa rana kan karin mafi karancin albashi a Najeriya, Farfesa Kemi Okuwa ta Cibiyar Nazarin Zamantakewa da Tattalin Arziki ta Najeriya (NISER), ya bayyana cewa kasar ce ta 44 a Afirka wajen biyan mafi karancin albashi.
Har yanzu dai ana kai ruwa rana tsakanin kungiyar kwadago da gwamnatin kasar kan sabon mafi karancin albashi.
Hasali ma, ana ja-in-ja tsakanin matakan gwamnatin kasar uku, domin kuwa jihohi da kananan hukumomi na cewa ba za su iya biyan sabon albashin N62,000 da gwamnatin tarayya take so ba.
Kungiyoyin kwadagon Najeriya dai sun dade da yin watsi da karin mafi karancin albashin zuwa N62,000 da gwamnatin tarayya ta yi.
Duk kuwa da cewa kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) da kungiyar kananan hukumomin Najeriya (ALGON) sun ce ba za su iya biyan wannan adadi ba.
Wani abin ban mamaki, kungiyar kwadagon ta ce ba za ta amince da duk abin da ya gaza N250,000 a matsayin mafi karin albashin da ma’aikata ba.
Masana da dama da masu tsokaci, ciki har da wasu ’yan majalisar dokokin kasar na ganin kara mafi karancin albashin zuwa N100,000 zai daukaka rayuwar ma’aikata ba tare da haifar da karin hauhawar farashin kayayyaki da zai kara yin illa ga tattalin arzikin kasar ba.
Ma’aikata miliyan 5.3 ne za su amfana
Najeriya mai yawan al’umma miliyan 229, na da yawan ma’aikata miliyan 76, amma ba dukkan ma’aikatan ne kai tsaye za su samu karin albashi ba saboda wasu dalilai, in ji manazarta.
A yayin da masana ke ganin cewa ma’aikatan gwamnati sun fi cancantar karin fuskar albashi, amma sun lura cewa idan gwamnati na son magance matsalar albashin da ake fama da shi a kasar nan, dole ne duk matakan gwamnati su kara kaimi wajen rage tsadar rayuwa.
Dole ne kuma su samar da yanayin da za su iya bunkasa harkokin kasuwanci, wanda hakan zai inganta rayuwar miliyoyin ’yan kasa da ke cikin fatara.
Masana dai na ganin cewa da yawa daga cikin ma’aikatan gwamnati na karbar bashi ko kuma amfani da wasu hanyoyin haram wajen samun karin kudaden shiga domin su iya biyan bukatun rayuwa na abinci, matsuguni, lafiya, ilimi da sufuri da dai sauransu.
Mafi karancin albashin ma’aikatan gwamnatin tarayya, wanda a halin yanzu yake N30,000, an kara shi ne a shekarar 2019, lokacin da hauhawar farashin kayayyaki ya kasance tsakanin kashi 11 zuwa 12%.
Sai dai kuma yanzu darajar Naira ta ragu da kashi 276% cikin dari idan aka kwatanta da yadda take a 2019.
Hakan na daga cikin dalilan neman inganta tsarin albashi.