Ma’aikata sun yi watsi da shirin cire tallafin kudin man fetur

Kungiyar ma’aikata ta yi watsi da shirin gwamnnati na cire tallafin kudin man fetur da kuma kara harajin da ake biya akan kayan da mutane suke saye yau da kullum (VAT) a yayin da suka bukaci kasar da ta sake bin diddigin taswirar tsaron kasar. Kungiyar ta bayyana hakan ne a yau Laraba a dandalin […]

Ma’aikata sun yi watsi da shirin cire tallafin kudin man fetur

Kungiyar ma’aikata ta yi watsi da shirin gwamnnati na cire tallafin kudin man fetur da kuma kara harajin da ake biya akan kayan da mutane suke saye yau da kullum (VAT) a yayin da suka bukaci kasar da ta sake bin diddigin taswirar tsaron kasar.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a yau Laraba a dandalin filin taro na Eagle Square a Abuja. Kungiyar ta ce, karin kudin harajin VAT da kudin man fetur zai kara radadin talauci a Najeriya.

Shugaban kungiyar kwadagon Najeriya (NLC), Ayuba Wabba da shugaban kungiyar (TUC), Bobboi Bala Kaigama ne suka hadu wajen yi wa ma’aikatan jawabi. Taron ya samku halartar mataimakin shugaban Najeriya  Yemi Osinbajo wanda ya wakilici shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, da dubban ma’aikatan gwamnati.