Ma’aikatan Abuja ba sa sona — Wike
Hakan ya faru ne sakamakon rage kashe kuɗi kan tafiye-tafiye da taruka, tare da karkatar da kuɗaɗen zuwa ayyukan raya ƙasa.
Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike ya ce ya san baida da farin jini a wajen ma’aikatan gwamnati saboda matakan da yake ɗauka.
Hakan ya faru ne sakamakon rage kashe kuɗi kan tafiye-tafiye da taruka, tare da karkatar da kuɗaɗen zuwa ayyukan raya ƙasa.
- Boko Haram sun kai hari sansanin sojoji da ofishin ’yan sanda
- Gwamnati ta ƙara albashin sojoji — Ministan Tsaro
Da yake magana a taron manema labarai na wata-wata da ya gudanar a Abuja, Wike ya ce ba zai amince da kashe miliyoyin Naira wajen tura jami’ai taruka a ƙasashen waje ba, musamman idan ana iya samun irin wannan ƙwarewa a cikin Najeriya.
Ya ce, gwamnatinsa ta sauya tsarin kasafin kuɗi, inda yanzu kashi 70 cikin 100 ake ware wa ayyukan raya ƙasa, yayin da kashi 30 cikin 100 kaɗai ake kashewa wajen tafiyar da gwamnati.
Ministan ya kuma yi zargin cewa wasu taruka da ake halarta a baya sun zama hanyar karkatar da kuɗaɗen gwamnati, yana mai cewa ya fi dacewa a zuba irin waɗannan kuɗaɗe wajen gina tituna da sauran ayyukan da jama’a za su amfana da su kai tsaye.
Ya ce, wannan ne ya sa ma’aikatan gwamnati da dama ba sa son shi, amma ya jaddada cewa abin da ya fi muhimmanci a gare shi shi ne gudanar da ayyukan da za su amfani al’umma.