Ma’aikatan asibiti 3 sun shiga hannu kan satar jarirai
Ma’aikatan asibitin uku sun shiga hannu bayan mika rahoton zarginsu da satar jariran.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ebonyi ta cafke wasu ma’aikatan Asibitin Koyarwa na Jami’iar Alex Ekwueme da ke Abakaliki kan zarginsu da satar jarirai.
Kakakin ’yan sandan Jihar, Loveth Odah, ce ta tabbatar da cafke su, inda ta ce an gano jarirai biyu mace da namiji a hannun wadanda ake zargin.
- An yi jana’izar dan majalisar Kadunan da ’yan bindiga suka kashe
- Kotu ta tsare matar da ta karya ’yar mijinta da tabarya a Sakkwato
Ta kuma ce wadanda ake zargin sune Ndidiamaka Enyinta Emeka da Chinenye Idam da kuma Maryjane Inya.
Loveth ta ce an kama wadanda ake zargin tun a ranar 10 ga watan Disamban 2021, bayan korafi da aka kai wa ’yan sandan cewa an ga Maryjane da wasu jarirai kuma ana kyautata zaton na sata ne.
Kakakin ’yan sandan ta ce tuni aka mika su zuwa ga Sashen Binciken Manyan Laifuka na hidekwatar rundunar, don fadada bincike a kansu.