Ma’aikatan Babban Bankin Najeriya sun sace Naira biliyan 8
Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta gurfanar da wasu manyan jami’an Babban Bankin Najeriya (CBN) a gaban kotu bisa zarginsu da yin zambar kusan Naira biliyan takwas. Hukumar EFCC ta ce manyan jami’an bankin na CBN su shida tare da wasu jami’an bankunan kasuwanci su 16 sun hada baki ne wajen […]

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta gurfanar da wasu manyan jami’an Babban Bankin Najeriya (CBN) a gaban kotu bisa zarginsu da yin zambar kusan Naira biliyan takwas.
Hukumar EFCC ta ce manyan jami’an bankin na CBN su shida tare da wasu jami’an bankunan kasuwanci su 16 sun hada baki ne wajen yin zambar wadannan makudan kudi ta hanyar sauya adadin wasu tsofaffin kudi da suke kula da su.
Jami’an su 22 an gurfanar da su ne a gaban Alkalin Babbar Kotun Tarayya da ke Ibadan babban birnin Jihar Oyo Mai shari’a Ayo Emmanuel.
Jami’an shida sun hada da Misis Patience Okoro Eye da Afolabi Olufemi da Kolawole Babalola da Olaniran Muniru Adeola da Fatai Yusuf Adekunle da kuma Ilori Adekunle Sunday. Ana zarinsu da yin badakalar tsofaffi da yagaggun kudi a jihohi da dama na kasar nan, inda ake tuhumarsu da laifuffuka biyar da suka hada da hadin baki da damfara da kuma sata.
Ana zargi ma’aikatan Babban Bankin da kin yin aiki da umarnin Babban Banki na lalata wasu manyan takardun kudi tare da dakile hauhawar farashi. Kuma maimakon su lalata takardun kudin an zarge su da sake dawo da kudin don amfani da su tare da maye gurbinsu da wasu takardu da aka yanka daidai da girman Naira.
Lokacin da aka karanta musu abin da ake zarginsu da shi, mutanen shida sun musanta zargin.
Tuhuma ta farko na cewa: “Ke Patience Okoro Eye da Afolabi Olufemi Johnson da Ilori Adekunle Sunday da Kolawole Babalola da Olaniran Muniru Adeola da kuma Fatai Adedokun Yusuf a ranar 5 ga Agusta, shekarar 2014 a Ibadan da ke karashin hurumin wannan kotu kun yi amfani da mukamanku a matsayinku na ma’aikatan Babban Bankin Najeriya kuka jawo wa tattalin arzikin Najeriya illa, lokacin da kuka lalata wasu akwatuna da aka yi musu maki da “kidayayyun Kudi Masu Dauda da aka tantance” alhali cike suke da jaridu maimakon akwatuna masu dauke da Naira miliyan 10 na takadrun Naira dubu, lamarin da ya jawo karuwar kudi da ke karakaina a tsakanin jama’a wanda hakan ya saba wa manufar Babban Bankin Najeriya na takaita yawan kudi a hannun jama’ wanda yin hakan ya saba wa sashi na 1(2) (b) da sashi na 10 (1) na dokar kwato dukiyar jama’a (Tanadi na Musamman) na doka mai lamba, Cap R4, na dokokin Najeriya na shekarar 2014.”
Tuhuma ta biyu ta ce: “Ke Patience Okoro Eye da Afolabi Olufemi Johnson da Ilori Adekunle Sunday da Kolawole Babalola da Olaniran Muniru Adeola da kuma Fatai Adedokun Yusuf a ranar 5 ga Agustan 2014, a Ibadan da ke karkashin hurumin wannan kotu, kun aikata almundahana lokacin da kuka sauya takardun Naira dubu-dubu da suka kai Naira miliyan 10 da aka yi musu maki da “kidayayyun Kudi Masu Dauda” da aka tsara lalata su amma kuka musanya su da takardun jarida tare da mayar da wadancan kudi don amfanin kanku, wanda haka kun aikata laifin da za a iya hukunta ku a karkashin sashi na 1(2) (a) da sashi na 10 (1) na dokra kwato dukiyar jama’a (Tanadi na Musamman) mai lamba Cap R4, na dokokin Najeriya na shekarar 2014.”
Mai gabatar da kara, Rotimi Jacobs, SAN, ya roki kotun ta sanya ranar fara sauraron shari’ar tare da bukatar a sakaye wadanda ake zargin a gidan maza. Ya ki amincewa da batun bayar da beli gare su, inda ya bukaci lauyansu ya rubuto bukatar belin kamar yadda doka ta tanada.
Lauyan wadda ake zargi ta farko K. A. Lawal ya gabatar da bukatar beli da fatar baki, inda sauran lauyoyin suka biyo bayansa.
Mai shari’a Emmanuel ya dage zaman kotun zuwa ranar 9 ga Yuni domin duba batun beli, inda ya sanya ranar 6 da 7 ga Yuli mai zuwa domin fara sauraron shari’ar. Kuma ya bayar da umarnin a tsare dukkan wadanda ake zargi a kurkukun Agodi da ke Ibadan.