Ma’aikatan jinya 300 na cikin hadarin kamuwa da Coronavirus a Lagos
Kungiyar ma’aikatan jinya ta Najeriya reshen jihar Legas ta bayyana cewa sama da ma’aikatan jinya 300 ne ke cikin hadarin kamuwa da cutar coronavirus a Legas. A cewar kungiyar, zuwa yanzu 16 daga cikin ma’aikatan jinyar sun an tabbatar da sun kamu da cutar yayin da 4 daga cikin su suka warke aka sallame su. […]
Kungiyar ma’aikatan jinya ta Najeriya reshen jihar Legas ta bayyana cewa sama da ma’aikatan jinya 300 ne ke cikin hadarin kamuwa da cutar coronavirus a Legas.
A cewar kungiyar, zuwa yanzu 16 daga cikin ma’aikatan jinyar sun an tabbatar da sun kamu da cutar yayin da 4 daga cikin su suka warke aka sallame su.
Kungiyar ta shaida haka ne a shafin ta na twitter @LagosNannm, inda ta bayyana cewa ma’aikatan jinya sama da 300 sun sami kan su ne cikin halin hadarin kamuwa da cutar ne a lokacin da suke bakin aiki.
Ta ce, ma’aikatan lafiya da ke kan gaba wajen dakile cutar Coronavirus, kwararru ne da cutar ta cinmmasu a lokacin da suke gudanar da aiyukansu.
A saboda haka tayi kira ga ‘yan Najeriya da su sanya su a addu’a.
Tun a baya dai, kungiyar ta yi kira ga ma’aikatan jinyar a Legas da su kasance masu kiyaye wa a lokacin da suke a bakin aiki.
” Tabbas aikin na yiwa kasa da al’umar ta hidima ne, amma duk da haka bai kamata ku dinga jefa rayuwar ku da ta masoyan ku cikin hadari ba, idan ba a tanadar maku da kayan kariya na aiki ba, kuma ta yi du bi kan hanyoyin da suka dace ku nema a baku, kafin ku duba marasa lafiya.” Inji sanarwar kungiyar.
Sanarwar ta kara da cewa, ma’aikatan jinya nada hurumin kin duba marasa lafiya idan ba a tanadar masu kayan aiki na kare kansu ba.