Ma’aikatan jinya sun koka kan rashin albashin watanni 8 a Kaduna
An ba mu albashin watanni uku amma na sauran watanni takwas sun maƙale.
Sabbin ma’aikatan jinya da ungozoma da aka ɗauka aiki a Jihar Kaduna sun yi kira ga Gwamna Uba Sani da ya sa baki a kan rashin biyan albashinsu na watanni takwas.
Sama da ma’aikatan lafiya 200 gwamnatin jihar ta ɗauka a watan Yunin 2023 a kan matakin albashi na 7 kuma aka tura su zuwa manyan asibitocin jihar.
- Kotu ta dakatar da NERC da KEDCO daga ƙarin kuɗin wutar lantarki
- Yaƙin Gaza: Turkiyya ta dakatar da harkokin kasuwanci da Isra’ila
Aminiya ta samu rahoton cewa ma’aikatan jinyar sun yi aiki na tsawon watanni ba tare da an biya su albashi ba.
Sai dai a kwanan baya an biya su albashin watan Fabarairu da Maris da Afrilu yayin da albashin sauran watanni takwas ɗin suka maƙale.
Wasu daga cikin ma’aikatan jinyar da abin ya shafa sun yi ikirarin cewa an cire masu wasu kuɗi a cikin albashinsu na Fabarairu da Maris da Afrilu, saɓanin adadin da aka rubuta a takardun ɗaukar aikinsu ba tare da wani bayani daga ma’aikatar ba.
Ɗaya daga cikin ma’aikatan jinyar wacce ta bayyana sunanta da Ummul Tani saboda tsoron kada a yi mata barazana, ta ce, “Ba a biya mu bashin albashin watanni takwas da muka yi aiki ba.
“Saboda mun fara aiki a watan Yunin 2023 amma mun fara karɓar albashi daga watan Fabrairun 2024.
“Muna da mata masu aure da waɗanda aka sake su a cikinmu waɗanda ke kula da kansu da kuma ’ya’yansu.
“Dole ne mutum ya tsaya ya yi tunanin irin damuwar da za su shiga ko don sauke nauyin da rataya a wuyansu na iyalansu.”