Ma’aikatan jinyar masu COVID-19 sun tafi yajin aiki

Ma’aikatan lafiya da ke kula da masu cutar coronavirus a cibiyar killace masu cutar da ke Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH) sun tafi yajin aiki. A sakamakon haka masu dauke da cutar su19 da ke kwance a cibiyar na zaune babu masu kula da lafiyarsu. Ma’aikatan na yajin aikin ne saboda rashin rashin samar […]

Ma’aikatan jinyar masu COVID-19 sun tafi yajin aiki

Wata cibiyar killace wadanda suka kamu da coronavirus mai gado 300 da ake aikin kafawa a Abuja (Hoto: Kola Sulaimon / AFP)

Ma’aikatan lafiya da ke kula da masu cutar coronavirus a cibiyar killace masu cutar da ke Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH) sun tafi yajin aiki.

A sakamakon haka masu dauke da cutar su19 da ke kwance a cibiyar na zaune babu masu kula da lafiyarsu.

Ma’aikatan na yajin aikin ne saboda rashin rashin samar masu da wuraren kwana da kuma kin biyan kudaden alawus dinsu.

Hujjar kungiyar ma’aikatan na shiga yajin aiki.

Da take tabbatar da hakan, shugabar Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya Reshen JUTH, Misis Mercy Lenka ta dora laifin a kan Gwamnatin jihar Filato.

Ta ce sun tafi yajin aikin ne domin tseratar da ‘ya’yan kungiyar daga kamuwa da cutar coronavirus.

“Mun umarci ‘yan kungiyarmu su kaurace wa cibiyar killace masu cutar coronavirus, domin bai kamata duk mai cudanya da masu cutar ya koma gida ya ci gaba da mu’amala da iyalensa ba.

Abin da ya kamata da kokarin da kungiyar ta yi.

“Ya kamata gwamnati ta samar wa ma’aikatanmu wurin zama, bayan sun dawo daga wajen aiki.

“Kuma su zauna a wajen har na tsawon makonni biyu a wurin bayan sun kammala aiki. Sannan a gwada su a tabbatar ba su dauke da wannan cuta kafin su koma cikin iyalensu.”

Amma ta ce ba a tanadar musu da komai ba sannan ba a ba su komai na kudaden alawus dinsu ba, duk da hadarin da rayukansu ke shiga a wurin jinyar masu cutar.

Ta kara da cewa sun yi iya kokarinsu na jayo hankalin gwamnati kan muhimmancin magance matsalolin amma ba su sami nasara ba.

Don haka suka shiga yajin aikin ganin irin hadarin da su da iyalensu ke ciki, har zuwa sadda za a warware matsalolin nasu.

Me gwamnatin Filato ta yi don magance matsalar?

Da aka tuntubi kwamishinan lafiya na jihar Filato, Dokta Ninkong Lark kan wannan al’amari, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta yi nisa wajen magance matsalolin.

Ya ce an sami wurin ajiye ma’aikatan lafiyan a sansanin hukumar  NDLEA da ke garin Jos.

Kwamishinan yi roki ma’aikatan su koma bakin aiki, domin an riga an samar masu wuraren kwana. Kuma su tuna cewa marasa lafiyan ‘yan uwansu ne ‘yan Jihar Filato.

Hukumar asibitin JUTH.

A nata bangaren Jami’ar Hulda da Jama’a ta asibitin, Misis Omini Bridjet ta zargi ma’aikatan da rashin bin matakan da suka kamata ba kafin su tafi fara yajin aiki.

“Ya kamata kafin su tafi yajin aikin su zauna da hukumar asibitin su bayyana matsalolin da suke damunsu. Amma ba su yi haka ba sai kawai muka ji labarin cewa sun tafi wannan yajin aiki,” a cewarta.