Ma’aikatan Kaduna sun yi watsi da yajin aikin kungiyar kwadago
Ofisoshin gwamnatin jihar Kaduna sun ci gaba da ayyukansu kamar kullum duk da sanarwar yajin aikin gama gari da kungiyar kwadago ta fara a yau Alhamis. An dai fara yajin aikin gama garin ne bayan da gwamnatin Tarayyar Najeriya taki amincewa akan batun sabon albashi mafi karanci ga ma’aikatan kasar. Majiyar kamfanin dillancin labarai NAN […]

Ofisoshin gwamnatin jihar Kaduna sun ci gaba da ayyukansu kamar kullum duk da sanarwar yajin aikin gama gari da kungiyar kwadago ta fara a yau Alhamis.
An dai fara yajin aikin gama garin ne bayan da gwamnatin Tarayyar Najeriya taki amincewa akan batun sabon albashi mafi karanci ga ma’aikatan kasar.
Majiyar kamfanin dillancin labarai NAN ta ce, wakilinta ya ziyarci wasu ofisoshin jihar inda ya same su a bude su na ci gaba da gudanar da harkokinsu kamar yadda suka saba, wurare irin su: hadkwatar tara kudaden haraji (Obasanjo House) da Sakatariyar gwamnati na ci gaba da ayyukansu.
Wuraren ayyuka kamar: wasu bankuna da makarantu da asibitoci da reshen babban bankin Najeriya CBN da sauran ofisoshin gwamnati duk su na bude.