Ma’aikatan Kamfanin New Nigerian sun janye yajin wata 31
Gamayyar kungiyoyi ma’aikatan Kamfanin Buga Jaridun New Nigerian da Gaskiya Ta Fi Kwabo da ke Kaduna sun janye yajin aikin da suka shafe wata 31 da suka faro a ranar 22 ga Janairun shekarar 2013.Wata sanarwa dauke da sanya hannun Shugaban kungiyar ’Yan jarida (NUJ) reshen kamfanin Abdull-Azeez Ahmed Kadir da na Ma’aikatan dab’i (NUPPPPROW) […]
Gamayyar kungiyoyi ma’aikatan Kamfanin Buga Jaridun New Nigerian da Gaskiya Ta Fi Kwabo da ke Kaduna sun janye yajin aikin da suka shafe wata 31 da suka faro a ranar 22 ga Janairun shekarar 2013.
Wata sanarwa dauke da sanya hannun Shugaban kungiyar ’Yan jarida (NUJ) reshen kamfanin Abdull-Azeez Ahmed Kadir da na Ma’aikatan dab’i (NUPPPPROW) Bulus Shabayan, ta ce ma’aikatan sun yanke shawarar janye yajin aikin ne bayan taron da suka gudanar da mahukuntan kamfanin da hadin gwiwar kungiyar kwadago (NLC) ta Jihar Kaduna inda suka yanke shawarar komawa bakin aiki a ranar Talatar da ta gabata don ba sababbin gwamnonin jihohin jihohin Arewa 19 da suke mallakar kamfanin a karkashin Shugaban Majalisar Gwamnonin Arewa Gwamna Kashim Shettima na Jihar Borno damar tattaunawa da sanin alkiblar da za a fuskanta.
Sanarwar ta ce, ma’aikatan kamfanin suna fata sabuwar majalisar gwamnonin arewar za ta zamo mai kazar-kazar wajen sake farfado Kamfanin NNN tare da nuna kula da hakkokin ma’aikatansa, domin kare martabar kamfanin da Sardaunan Sakkwato Sa Ahamdu Bello ya kafa.
Ma’aikatan sun nuna damuwa kan duk da dimbin kadarorin kamfanin amma ya shiga halin ni’yasu a ’yan shekarun bayan nan, inda suka bukaci gwamnonin Arewa su dauki matakan da suka wajaba wajen ceto kamfanin.
kungiyoyin sun yanke shawarar cewa ba za su lamunci a musguna wa wani ma’aikaci sakamakon janye yajin aiki, inda suka bukaci mahukuntan kafmanin su hanzarta fara biyan albashi mafi karanci na Naira dubu 18 da suka yi alkawari.
Sai sanarwar ta bukaci ma’aikatan kamfanin su kasance masu bin doka da oda tare da tsare ka’idojin aiki na kamfanin.