Ma’aikatan kananan hukumomi sun koka kan rashin biyandu albashi a kan lokaci
Kungiyar Ma’aikatan Kananan Hukumomi ta Kasa (NULGE) reshen Jihar Kaduna, ta koka kan rashin biyansu albashi a kan lokaci a Jihar Kaduna. Shugaban Kungiyar NULGE na Karamar Hukumar Chikun Danis Audu ne ya yi koken lokacin ziyarar ba-zata da Kwamishinan Kananan Hukumomi, Jafaru Ibrahim ya kai karamar hukumar. “Muna kira ga kwamishina ya taimaka wajen […]
Kungiyar Ma’aikatan Kananan Hukumomi ta Kasa (NULGE) reshen Jihar Kaduna, ta koka kan rashin biyansu albashi a kan lokaci a Jihar Kaduna.
Shugaban Kungiyar NULGE na Karamar Hukumar Chikun Danis Audu ne ya yi koken lokacin ziyarar ba-zata da Kwamishinan Kananan Hukumomi, Jafaru Ibrahim ya kai karamar hukumar. “Muna kira ga kwamishina ya taimaka wajen ganin an magance rashin biyan albashin ma’aikatanmu a kan lokaci tare da samar mana da issassun kujeru a ofishohin kananan hukumomi,” inji shi.
A jawabins Kwamishina Jafaru Ibrahim ya tabbatar wa ma’aikatan cewa ma’aikatarsa tana kokarin magance wannan matsala ta rashin samun albashinsu a kan kari.
Ya yi amfani da wannan dama wajen sanar da Kungiyar NULGE da ma’aikatan da ke wajen cewa a watan nan za a fara biyansu sabon albashin mafi karanci na Naira dubu 30, kamar yadda Gwamna Nasir El-Rufa’i ya sanar.
Don haka ya bukaci ma’aikatan jihar su saka wa Gwamnatin Jihar wajen tabbatar da suna zuwa aiki a kan lokaci tare da gudanar da ayyukansu yadda ya kamata domin ci gaban jihar.
Kwamishinan da ayarinsa sun kai irin wannan ziyara a Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu inda ya yaba da yadda ake gudanar da ayyuka cikin natsuwa.
Ya kuma bayyana niyyarsa ta ziyartar sauran kananan hukumomin jihar baki daya nan gaba.