Ma’aikatan lafiya sun fara yajin aiki

Daga Lahadi 13 ga watan Satumba, 2020 yajin aikin zai fara aiki.

Ma’aikatan lafiya sun fara yajin aiki

Hadaddiyar Kungiyar Ma’aikatan Lafiya ta Najeriya (JOHESU) ta ce za ta fara yajin aiki daga ranar Lahadi 13 ga Satumba, 2020.

Kungiyar ta ce yajin aikin ya zama wajibi saboda Gwamnatin Tarayya ta kasa biyan bukatun kungiyoyin ma’aikatan lafiyan da ke karkashinta.

“Daga 12 na dare ranar Lahadi, 13 ga Satumba, 2020 ’ya’yan kungiyarmu za su fara yajin aiki saboda gazawar Gwamnatin Tarayya ta biya bukatunmu”, a cewar sanarwar.

Shugaban kungiyar, Biobelemoye Josiah, ya ce taron kungiyoyin ma’aikatan lafiya da ke karkashin JOHESU sun yi ittifakin fara yajin aikin.

A baya ma’aikatan lafiyan sun ba wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwana 15 ta biya bukatun ma’aikatan lafiyan ko su tsunduma yajin aiki.

“Sakamakon haka ne babban Taron Majalisar Zartarwarmu ya yanke hukuncin fara yajin aikin saboda babu wani kwakkwaran abun da aka cimma a ganawarmu da Gwamnantin Tarayya”, kamar yadda kungiyar ta bayyana.