Ma’aikatan man fetur sun fara yajin aiki

Ma’aikatan man fetur da iskar gas a Najeriyar sun shiga yajin aikin gargadi na kwana uku. Kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas (PENGASSAN) ta ce tana yajin aikin ne saboda rashin biyan ‘ya’yana albashi na tsawon wata uku da kuma sanya su cikin tsarin albashi na bai-daya (IPPIS). Mai magana da yawu PENGASSAN, Injiniya […]

Ma’aikatan man fetur sun fara yajin aiki

Ma’aikatan man fetur da iskar gas a Najeriyar sun shiga yajin aikin gargadi na kwana uku.

Kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas (PENGASSAN) ta ce tana yajin aikin ne saboda rashin biyan ‘ya’yana albashi na tsawon wata uku da kuma sanya su cikin tsarin albashi na bai-daya (IPPIS).

Mai magana da yawu PENGASSAN, Injiniya Fortune Obi  ya ce ma’aikatun da yajin aikin ya shafa su ne hukumar kayyade farashin albarkatun mai (PPPRA) da hukumar makamashin nukiliya ta (NNRA) da cibiyar horo kan albarkatun mai (PTI) da kuma hukumar kula da albarktun mai (DPR).

Kungiyar ta sanar da fara yajin aikin nata ne a ranar Laraba a hedikwatar ma’aikatar albakatun mai ta kasa da ke Abuja.