Ma’aikatan NAFDAC sun tsunduma yajin aiki
Ma’aikatan sun koka kan gazawar NAFDAC wajen biya musu buƙatunsu.
Ƙungiyar Ma’aikatan Manyan Hukumomi da Kamfanonin Gwamnati (SSASCGOC), wadda ke ƙarƙashin TUC, ta fara yajin aiki a Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC).
Wannan yajin aikin ya biyo bayan gazawar shugabancin NAFDAC wajen magance matsalolin da suka shafi jin daɗin ma’aikata.
- ’Yan bindiga sun sace shugaban makaranta da wasu 8 a Kaduna
- ’Yan Boko Haram sun fara ɓuya a sansanonin ’yan gudun hijira – Zulum
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar 4 ga watan Oktoba, 2024, ƙungiyar ta bayyana cewa an fara yajin aikin ne bayan tattaunawa da shugabancin NAFDAC.
Sanarwar ta ce sun buƙaci ƙarin girma, albashi, da jin daɗin ma’aikata, amma ba su samu sakamakon da suka buƙata ba.
Sanarwar, wadda Sakataren TUC, Kwamared Ejor Michael ya sanya wa hannu, ta umarci ma’aikatan da su fara yajin aikin daga ranar Litinin, 7 ga watan Oktoba.
Ƙungiyar ta ce, “Mun sanar da shugabancin NAFDAC a ranar 20 ga watan Satumba, 2024, inda muka ba su wa’adin kwana 14 su magance matsalolinmu.
“Tun da ba su yi komai ba, mun sake yin wani taro a ranar Juma’a, 4 ga watan Oktoba, 2024. Bayan tattaunawa, mun yanke shawarar fara yajin aiki a ƙasa baki ɗaya daga ranar Litinin, 7 ga watan Oktoba.”
Ƙungiyar ta umarci ma’aikatan su dakatar da aiki tare da ɗauke kayayyakinsu daga ofisoshi saboda ba za a bari kowa ya shiga ofisoshin NAFDAC ba yayin da ake yajin aiki.
Ta kuma umarci shugabannin SSASCGOC na jihohi da yankuna su tabbatar da cewa ma’aikata sun bi umarnin shiga yajin aikin.