Ma’aikatan Najeriya ba su taɓa shiga mummunan yanayi haka ba —Atiku

Duk da tsawaita alƙawuran da gwamnati ta yi, amma maganar ƙarin albashi ga ma’aikacin Najeriya ta kasance abin takaici.

Ma’aikatan Najeriya ba su taɓa shiga mummunan yanayi haka ba —Atiku

Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban Ƙasa Atiku Abubakar ya jajanta ma ma’aikatan Najeriya, inda ya ce sun yi aiki da gwamnati tare da tsare-tsaren da suka saɓa wa rayuwarsu.

Ya bayyana hakan ne a saƙon Ranar Ma’aikata ta Duniya ga ma’aikatan Najeriya.

Atiku ya bayyana cewa yayin da suke tare da takwarorinsu na duniya domin bikin Ranar Ma’aikata Ta Duniya, “da gaskiya ce ta ɗore da yanzu halin da ma’aikacin Najeriya ke ciki ya sauya.”

Ya ce, “Duk da tsawaita alƙawuran da gwamnati ta yi, amma maganar ƙarin albashi ga ma’aikacin Najeriya ta kasance abin takaici.

“Kowane ma’aikaci yana shiga sabbin wahalhalu da matsanancin yanayin rayuwa.

“Bayan koma baya da saɓani da gwamnati ke yi na ko tsarin tallafin mai ya tafi ko kuma ana ci gaba da aiwatarwa, a yau ƙasar nan na fuskantar fushin ’yan Najeriya da ke ɓarnatar da lokutnsu masu daraja a dogayen layuka a gidajen mai a faɗin ƙasar nan.

“Tallafin man fetur ya tafi a yadda aka bayyana; amma duk da haka tasirinsa ya daɗe – yana nuna gazawar gwamnati mai ci a yanzu.

“A cikin wani yanayi da ba a taɓa ganin irinsa ba da kuma tauye haƙƙin ma’aikacin Nijeriya da sauran jama’a, wannan gwamnatin ta sanar da cire tallafin fetur ba tare da tuntuɓar wakilan ma’aikacin Nijeriya ba.

“An ci gaba da ƙarin kuɗin fito na ayyuka daban-daban ba tare da magance cin hanci da rashawa da rashin inganci.”

Tinubu ya dawo Abuja bayan halartar taro a Saudiyya

Zaɓen Ondo: Atiku ya gargaɗi INEC kan tafka maguɗin zaɓe

Sojoji sun tafka ƙazamin artabu da Bello Turji a Sakkwato 

Mutum 10 sun rasu a hatsarin mota a Jigawa