Ma’aikatan Najeriya sun fara yajin aiki yau

A safiyar yau Alhamis din nan kungiyoyin kwadagon Najeriya suka fara yajin aikin a fadin kasar. Wannan ya biyo bayan tashi baran-baran a tattaunawar da suka kai daren jiya suna yi da gwamnatin Tarayyar Najeriya akan akan batun sabon albashi mafi karanci ga ma’aikatan kasar. Ministan kwadagon Najeriya Chris Ngige ya gana da shugabannin kungiyar […]

Ma’aikatan Najeriya sun fara yajin aiki yau

A safiyar yau Alhamis din nan kungiyoyin kwadagon Najeriya suka fara yajin aikin a fadin kasar.

Wannan ya biyo bayan tashi baran-baran a tattaunawar da suka kai daren jiya suna yi da gwamnatin Tarayyar Najeriya akan akan batun sabon albashi mafi karanci ga ma’aikatan kasar.

Ministan kwadagon Najeriya Chris Ngige ya gana da shugabannin kungiyar a jiya Laraba inda ya bukaci kungiyar da ta janye yajin aikin zuwa 4 ga Oktoba 2018.

Bayan ganawar da Ministan ya yi da shugabannin kungiyoyin ya bayyana wa manema labarai cewa, zai gabatarwa gwamnatin tarayya bukatun kungiyoyin.