Ma’aikatan S-Power a Katsina murna ta koma ciki
Ga dukkan alamu murnar da wadansu matasa 2000 masu shaidar kammala Digiri da Gwamnatin Jihar Katsina karkashin Gwamna Aminu Bello Masari ta dauke su aikin koyarwa a makarantun gaba da firamare, kan albashin Naira dubu ashirin da biyar-biyar duk wata za ta koma ciki, lura da kwashe tsawon wata shida da fara aikin na wuccin-gadi […]
Ga dukkan alamu murnar da wadansu matasa 2000 masu shaidar kammala Digiri da Gwamnatin Jihar Katsina karkashin Gwamna Aminu Bello Masari ta dauke su aikin koyarwa a makarantun gaba da firamare, kan albashin Naira dubu ashirin da biyar-biyar duk wata za ta koma ciki, lura da kwashe tsawon wata shida da fara aikin na wuccin-gadi ba tare da samu albashin ko da wata daya ba.
Tun lokacin da Gwamnatin Masari ta dauke su aikin koyarwar mafi yawansu sun yi kallon hadari ne suka yi wanka da kashi. Sai ga shi har yanzu ruwan bai sauko ba. Basussukan da suka ci na kudaden tafiya wajen aiki da na abincin da suke bai wa iyali da wanda suke ci a wurin aikin sun kawo wuya har sun fara yin wasan buya a tsakaninsu da masu ba su bashin. Da fatan Gwamna Masari zai gaggauta biyansu hakkokinsu domin su inganta rayuwarsu. In kuma ya fitar da kudaden to ya sani sun makale a hanya sai ya bi sawu ya ga a ina ne suka makale?
Haruna MuhammadKatsina
Shugaban Kungiyar Muryar Jama’a
07039205659 Ko 08055887110