Ma’aikatan wutar lantarki sun yi barazanar sanya Najeriya a cikin duhu
Ma’aikatan wutar lantarki sun yi barazanar sanya Najeriya a cikin duhu matukar Gwamnatin Tarayya ta tilasta su yin aiki ba tare da biyansu hakkokinsu ba. Ma’aikatan sun bayyana haka ne ta bakin kungiyarsu ta kasa NUEE a ranar Litinin da ta gabata a garin Jos. Gwamnatin Tarayya dai ta yi alkawarin biyan ma’aikata dubu 40 hakkokinsu […]
Ma’aikatan wutar lantarki sun yi barazanar sanya Najeriya a cikin duhu matukar Gwamnatin Tarayya ta tilasta su yin aiki ba tare da biyansu hakkokinsu ba. Ma’aikatan sun bayyana haka ne ta bakin kungiyarsu ta kasa NUEE a ranar Litinin da ta gabata a garin Jos.
Gwamnatin Tarayya dai ta yi alkawarin biyan ma’aikata dubu 40 hakkokinsu gaba daya a wani bangare na sayar da kamfanonin wutar lantarki da suke karkashin Kamfanin Lantarki na kasa (PHCN) ga ’yan kasuwa.
Sakatare Janar na kungiyar NUEE Mista Joe Ajuero ne ya bayyana niyyar kungiyar lokacin taron manema labarai bayan ya yi jawabi ga ma’aikatan a ofishin kungiyar na shiyya da ke Jos kan fansho da garatutinsu da ba a biya ba.
Mista Ajuero ya yi zargin cewa Gwamnatin Tarayya ta yi barazanar yin amfani da sojoji da sauran jami’an saro wajen korar ma’aikatan Kamfanin PHCN daga ofisoshinsu a sassan kasar nan. “Muna rokon a biya mu hakkokinmu ne kawai, kafin mu bar ofisoshin, amma idan ba a biya mu ba, ba za mu bar sub a, kuma bai kamata a dakatar da biyanmu albashinmu ba,” inji shi.
Ya ce “Da zarar an biya mu kudinmu duka, za mu bar su ba tare da wani korafi ba. Amma idan suka ce za su yi amfani da masu dauke da makamai a kanmu, za mu jefa kasar nan a cikin duhu.”
Shiyyar Jos na Kamfanin PHCN ya kunshi jihohin Filato da Benuwai da Bauchi da Gombe, kuma fie da ma’aikata dubu uku ne suka halarci taron.
Mista Ajuero ya ce bayanan da jami’an gwamnati ciki har da Ministan Labarai, Labaran Maku cewa an biya mafi yawan ma’aikatan karya ce. Ya bayyana Minista Maku da Ministan “shara karya” inda ya bukaci a kore shi daga mukaminsa.
Mista Ajuero ya ce kasa da kashi 40 cikin 100 na ma’aikatan lantarki ne aka biya su garatuti ba are da fansho ba. “Amma babu ma’aikacin da aka biya shi fanshonsa,” inji shi.
Shugaban ya ce NUEE ba za ta bari a mika kamfanonin da aka sayar ga ’yan kasuwa ba, har sai an biya dukkan ma’aikatan hakkokinsu.