Ma’aikatan wutar lantarki sun yi yaji na gargadi a Gombe

A ranar Litinin din da ta gabata ne shugabaninin kungiyar Ma’aikatan Samar da Wutar Lantarki ta kasa (NUEE) reshen Jihar Gombe suka rufe ofisoshin Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Shiyyar Jos (JED) da ke jihar don nuna rashin amincewa da karin kudin wutar lantarki da aka yi wa abokan huldarsu.Da yake zantawa da manema labarai […]

Ma’aikatan wutar lantarki sun yi yaji na gargadi a Gombe
Ma’aikatan wutar lantarki sun yi yaji na gargadi a Gombe

A ranar Litinin din da ta gabata ne shugabaninin kungiyar Ma’aikatan Samar da Wutar Lantarki ta kasa (NUEE) reshen Jihar Gombe suka rufe ofisoshin Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Shiyyar Jos (JED) da ke jihar don nuna rashin amincewa da karin kudin wutar lantarki da aka yi wa abokan huldarsu.
Da yake zantawa da manema labarai a wajen ofishin kamfanin, Shugaban kungiyar NUEE na jihar, Kwamared Babangida Muhammad, ya nuna fushin kungiyar kan karin kudin wutar da kuma yadda ake korar ma’aikantansu ba bisa ka’ida ba.
Ya ce yanzu kamfanin ya yi karin kudin wutar lantarki da ya wuce misali kuma abokan huldarsu da suke da mita an daina daukar lissafin mitar an koma bai wa jama’a kiyasi, wadansu kuma idan mitar ta sha unit 100 sai a rubuta musu unit 300 kuma dole su biya.
Kwamared Babangida ya ce yanzu ofisoshinsu na shiyyar Arewa maso Gabas da Jos da Makurdi da Abuja da Legas duk an rufe su sai an cire wannan karin kudin wuta, inda ya gargadi masu amfani da wutar lantarki cewa kada su biya kudin sai an cire karin kuma an bai wa kowa mita mai kati kyauta.
Kwamared Babangida ya nuna bacin ransa kan yadda Kamfanin JED yake korar ma’aikata ba bisa ka’ida ba ko a dauko karamin ma’aikaci da bai san aiki ba a dora shi a kan na gaba da shi.
Ya ce wannan yaji na gargadi da suke yi yanzu idan ba a dauki mataki ba zai zama na sai baba-ta-gani inda za a fuskanci rashin wuta gaba daya.
Wadansu masu amfani da wutar lantarki da wakilinmu ya ji ta bakinsu Abubakar danjuma Bolari da Muhammad Hamisu da Usman Bello, sun koka kana bin da suka kira zaluntarsu da kamfanin na JED ke yi.
Sun ce addu’arsu ita ce Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya juyo kan kamfanonin wutar lantarki don kwato kamfanonin daga ’yan kasuwa ya mayar wa gwamnati.