Ma’aikatar Harkokin Neja Delta da NDDC za su hada hannu don raya yankin
Ma’aikatar Kula da Harkokin Neja-Delta (MNDA) da Hukumar Bunkasa Yankin Neja-Delta (NDDC) sun amince su hada hannu tare da daidaita ayyukansu domin cimman kudirin raya yankin.Ministan Harkokin Neja-Delta Dokta Stephen Oru ne ya bayyana haka a Fatakwal lokacin da ya kai ziyara hedkwatar Hukumar NDDC, inda shugaban hukumar da manyan jami’anta suka tarbe shi.Wata sanarwa […]
Ma’aikatar Kula da Harkokin Neja-Delta (MNDA) da Hukumar Bunkasa Yankin Neja-Delta (NDDC) sun amince su hada hannu tare da daidaita ayyukansu domin cimman kudirin raya yankin.
Ministan Harkokin Neja-Delta Dokta Stephen Oru ne ya bayyana haka a Fatakwal lokacin da ya kai ziyara hedkwatar Hukumar NDDC, inda shugaban hukumar da manyan jami’anta suka tarbe shi.
Wata sanarwa dauke da sanya hannun Daraktan Labarai, Malam Salisu Na’inna dambatta ta ruwaito Ministan yana cewa: “Makasudin wannan ziyara shi ne a karfafa hadin gwiwa a tsakanin Ma’aikatar Harkokin Neja-Delta da NDDC. Mun zo ne mu kara fahimtar irin ayyukan hukumar tare da nemo hanyoyin karfafa hadin kai domin cimma nasarar bunkasa yankin Neja-Delta.”
Dokta Oru ya ce, hukumar mai zaman kanta ce ba kamar yadda jama’a ke daukarta a matsayin bangare na ma’aikatarsa ba, sai dai akwai manufofin da suka yi tarayya a kai.
“Dukkan cibiyoyin wani kawo dauki ne na musamman na gwamnati da aka kafa su domin kawo ci gaba a bangaren inganta jin dadin jama’a da samar da kayan inganta rayuwa da tabbatar da zaman lafiya da bin doka,” inji shi.
Ministan wanda daraktocin ma’aikatar suka rufa wa baya, ya ce hada hannu a tsakanin ma’aikatar da hukumar zai kawar da maimaita abu guda a wajen aiki tare da takaita barnar dukiya kuma ya hanzarta kawo ci gaban yankin. “Bai kamata a rika ganin kamar muna cin dunduniyar juna ba. Wajibi ne mu rika aiki muna tuntuba da hadin gwiwa ta yadda za mu hada hannu wajen hanzarta kawo ci gaba a yankin kamar yadda ke kunshe cikin shirin Shugaban Goodluck Jonathan na sake fasalin kasa,” inji Ministan.
Ya bukaci a rika musayar ra’ayi da kwarewa a tsakanin sassan biyu, inda ya ce yankin Neja-Delta yanzu ya yi ban kwana da ’yan bindiga da zaman zauna-gari banza da satar jama’a da rashin bin doka da oda da sauran miyagun ayyuka.
Da yake mayar da jawabi Shugaban Hukumar Gudanarwar NDDC, Sanata Bassey Ewa Henshaw, ya amince da batun hada hannu da daidaita al’amura a tsakanin hukumarsa da ma’aikatar, inda ya ce hakan zai kai ga samar da babban ci gaba a cikin sauri wajen bunkasa yankin Neja-Delta.
“Muna matukar sha’awar yin aiki da ma’aikatar a wajen dabarun hada hannun,” inji shugaban hukumar.