Ma’aikatar Ilimi Ta Tarayya za ta bunkkasa Asusun TETFUND a Arewa maso Gabas
Ministan Ilimi Cif Ezenwo Nyesom Wike ya bayyana niyyar Gwamnatin Tarayya na inganta Asusun Tallafa wa Manyan Makarantu (TETFUND) ta samar da kudin da za su taimaka wajen kara bunkasa ilimi a shiyyar Arewa maso Gabas.Ministan ya bayyana haka ne a wurin taron masu ruwa da tsaki kan harkar ilimin manyan makarantu da ke shiyyar […]
Ministan Ilimi Cif Ezenwo Nyesom Wike ya bayyana niyyar Gwamnatin Tarayya na inganta Asusun Tallafa wa Manyan Makarantu (TETFUND) ta samar da kudin da za su taimaka wajen kara bunkasa ilimi a shiyyar Arewa maso Gabas.
Ministan ya bayyana haka ne a wurin taron masu ruwa da tsaki kan harkar ilimin manyan makarantu da ke shiyyar da aka gudanar a babban dakin taro na Jami’ar Abubakar Tafawa balewa da ke Bauchi a Litinin da ta gabata.
Minista Nyesom ya ja hankalin shugabannin makarantun su kara himma wajen yin ayyukan da suka dace domin bunkasa ilimi a yankunan. Ya ce sun kusa cimma burinsu wajen shawo kan yajin aikin da kwalejojin kimiyya da kere-kere na tarayya ta hanyar biya musu kashi 75 cikin 100 na bukatunsu, kuma nan ba da jimawa ba za a cimma matsaya.
Ministan ya ce Gwamnatin Tarayya ta samar da Naira biliyan 125 ga hukumomin ilimi a matakin farko na jihohin shiyyar daga shekarar 2010 zuwa 2013 domin tallafar ilimi.
Shugaban Kwamitin Amintattu na Asusun TETFUND Dokta Musa Babayo Talban Katagum ya bayyana kokarin gwamnatin ne wajen tallafa wa ilimi a karkashin asusun, inda ya nemi jagororin makarantun su himmatu wajen sauke nauyin da aka dora musu na samar da abubuwan da ake bukata a makarantunsu.
Shugaban Jami’ar Abubakar Tafawa balewa Farfesa Mohammed Hamisu Mohammed, ya yaba wa kokarin da gwamnatin ke yi a fannin ilimi, ya ce irin tallafin da asusun ke bayarwa ya taimaka wa makarantun shiyyar.