Ma’aikatar Muhalli za ta ba Jami’ar Ahmadu Bello irin itatuwa dubu 10

Babban Sakatariya a Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya Hajiya Fatima Nana Mede ta bayyana niyyar ma’aikatar ta tallafa wa Jami’ar Ahmadu bello da ke Zariya a bangarorin da suka shafi kokarin jami’ar na dasa itatuwa don kawatawa da kare muhalli.Sakatariyar ta bayyana haka ne a wajen bikin dashen itatuwa na bana da ya gudana a harabar […]

Ma’aikatar Muhalli za ta ba Jami’ar Ahmadu Bello irin itatuwa dubu 10
Ma’aikatar Muhalli za ta ba Jami’ar Ahmadu Bello irin itatuwa dubu 10

Babban Sakatariya a Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya Hajiya Fatima Nana Mede ta bayyana niyyar ma’aikatar ta tallafa wa Jami’ar Ahmadu bello da ke Zariya a bangarorin da suka shafi kokarin jami’ar na dasa itatuwa don kawatawa da kare muhalli.
Sakatariyar ta bayyana haka ne a wajen bikin dashen itatuwa na bana da ya gudana a harabar jami’ar da ke Samaru, inda ta ce ma’aikatar za ta taimaka wa jami’ar da irin dasawa guda dubu 10 tare da taimaka mata wajen bayar da horo kan yadda za a raini itatuwan da aka dasa.
Hajiya Fatima ta ce yadda koren ganye ke da daukar ido a harabar Jami’ar Ahmadu Bello ya nuna irin kokarin da mahukuntan jami’ar ke yi wajen kare muhallinsu saboda haka ta ce za su ci gaba da mara wa wannan kokari baya.
Tun farko a jawabin shugaban jami’ar Farfesa Ibrahim Garba ya ce, Jami’ar Ahmadu Bello ta dukufa wajen dashen itatuwa ne domin kawar da barazanar da muhalli ke fuskanta na zaizayar kasa da ambaliyar ruwa da kwararowar hamada.