Ma’aikatar noma na nuna wa makiyaya bambanci – Miyetti Allah

kungiyar kare muradu da al’adu na Fulani ta Miyetti Allah-Kautal hore ta zargi ma’aikatar noma ta tarayya karkashin jagorancin ministan ma’akatar, Cif Audu Ogbe da nuna wariya ga al’ummarsu inda ta yi zargin cewa ma’aikatar wadda sha’anin noma da kiwo ke karkashinta, da rashin nuna kulawa a kan bukatunsu sai dai na manoma kadai. Shugaban […]

Ma’aikatar noma na nuna wa makiyaya bambanci – Miyetti Allah

kungiyar kare muradu da al’adu na Fulani ta Miyetti Allah-Kautal hore ta zargi ma’aikatar noma ta tarayya karkashin jagorancin ministan ma’akatar, Cif Audu Ogbe da nuna wariya ga al’ummarsu inda ta yi zargin cewa ma’aikatar wadda sha’anin noma da kiwo ke karkashinta, da rashin nuna kulawa a kan bukatunsu sai dai na manoma kadai. Shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Abdullahi Bodejo ne ya bayyana korafin tare da sakatarenta na kasa, Injiniya Saleh Alhassan a yayin wata zantawa da ’yan jarida jim kadan bayan sun tattauna da daya daga cikin jagororin daya bangaren kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah mai lakabin “Cattle Breeders” Alhaji Haruna Garus Gololo.

kungiyoyin biyu sun koka a kan halin da makiyaya ke ciki musamman ma a jhar Benuwai bayan kafa dokar hana kiwo a jihar da kuma na jihar Taraba da ke shirin fara amfani da dokar inda su ka ce ma’aikatar ta gaza wajen samar masu da mafita sannan kuma ministan injita bai da sha’awar kyautata lamuran kiwo a aikace sabanin yadda ya ke ta yayatawa. 

A saboda haka inji kungiyoyin biyu su na bukatar gwamnatin tarayya da ta kafa wata hukuma mai karfi a karkashin ma’aikatar don kula da sha’anin kiwo da sauran bukatu na makiyaya.

Da ya ke amsa tambayar Aminiya a kan ko me ya sa sai a yanzu ne bangarorin biyu su ka yanke shawarar hada kai tare bayan zaman doya da manja a baya, kodinetan Miyetti Allah Alhaji Haruna Garus Gololo wanda a yayin kafa dokar ya bayyana goyon bayan bangarensu a kai, cewa ya yi ya goyi bayan kafa dokar ne a lokacin bayan gwamnan jihar ta Benuwai ya yi wa bangarensu alkawarin zai kafa wuraren kiwo uku tare da samar da ababan more rayuwa da ya hada da makaranta da mahauta a matsayin na gwaji, “Sai dai har lokacin kafa dokar gwamnan ya gaza cika alkawarinsa. Inji shi.

“Daga baya-bayan nan labarin da mu ka samu shi ne wani makiyayi a yankin Katsina-Ala da ke jihar ya rasa dabbobi sama da dari a sakamakon rashin abinci da ruwa bayan kakaba dokar sannan wani kuma  ya rasa ransa. 

Ba musan makomar daruwa masu irin wannar matsalar ba da kuma na dubban dabbobinsu, inji Garus Gololo.