Ma’aikatar Sufuri ta horar da ‘yan Keke NAPEP

Ma’aikatar ayyuka da sufuri ta jihar Filato ta kaddamar da shirin horar da masu tuka keke Napep, kan sanin dokokin tuki da hanya a garin Dadin kowa da ke kusa da Jos, babban birnin Jihar Filato. Da yake jawabi a lokacin yake kaddamar da wannan shiri, babban sakatare a ma’aikatar ayyuka da sufuri ta Jihar […]

Ma’aikatar Sufuri ta horar da ‘yan Keke NAPEP

Ma’aikatar ayyuka da sufuri ta jihar Filato ta kaddamar da shirin horar da masu tuka keke Napep, kan sanin dokokin tuki da hanya a garin Dadin kowa da ke kusa da Jos, babban birnin Jihar Filato.

Da yake jawabi a lokacin yake kaddamar da wannan shiri, babban sakatare a ma’aikatar ayyuka da sufuri ta Jihar Filato, Dokta Gabriel Danladi Mafulul ya bayyana cewa sun  shirya wannan taron horarwa ne,  don su horar da ’yan Keke Napep su nuna masu ka’idojin tafiya a kan hanya.

Ya  ce domin  suna ganin yadda  ‘yan Keke Napep suke tuki batare da bin ka’idar hanya ba. 

Ya ce wasu masu tukin Keke Napep suna tuki kamar yadda ake tukin babur. Domin ba su san cewa tukin Keke Napep, kamar tukin mota ne ba. 

Dokta Gabriel Danladi Mafulul ya yi bayanin cewa suna so a Filato duk wanda ya fita daga gidansa ya tafi lafiya ya dawo lafiya. Don haka suka fito da wannan shiri na horar da  ’yan Keke Napep  kan ka’idojin hanya.

Ya ce bayan wannan horarwa ma’aikatar za ta bai wa dukkan masu tuka keke Napep a jihar, lasin tuka keke Napep. Ya ce nan da karshen watan biyu duk wanda yake tuka keke Napep a Jihar Filato, da bai samu irin wannan horo da 

karbar takardar lasin na tuka keke Napep ba, jami’an tsaro za su kama shi.

Don haka ya yi kira ga dukkan masu tuka keke Napep da ke jihar su hanzarta zuwa su shiga wannan shiri, kuma su karbi takadar lasin na tuka keke Napep.

Shi ma a nasa jawabin shugaban kungiyar masu tuka keke Napep a Jihar Filato Kwamared Markus Yakubu ya bayyana cewa  gaskiya wannan shiri na horar da masu tuka Keke Napep da ma’aikatar ayyuka da sufuri ta Jihar Filato ta shirya musu ya yi daidai. 

Ya ce ya kamata duk sana’ar da mutum yake yi  ya martaba wannan sana’a, kuma ya san dokokin wannan sana’a.

 Ya ce don haka wannan aiki horarwa zai amfani ’yan keke Napep kwarai da gaske. Domin zai rage  halin ganganci a hanyoyi.

Ya yi kira  ga ‘yan wannan kungiya su baiwa  wannan shiri goyan baya da hadin kai.

 

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno