Ma’aikatu sun hana Musulmi yin azumi a China
Wasu ma’aikatun gwamnati a yankin dinjiang na yammacin kasar China sun hana al’ummar Musulmi yankin yin azumi a wannan watan na Ramadan.Wadanda aka hana su yin azumin galibinsu malaman makaranta ne da dalibai da kuma ma’aikatan gwamnati wadanda ’yan kabilar Uighur ne marasa rinjaye.Wata kungiyar ’yan kabilar ta Uighur ta ce wasu ma’aikartun suna ba […]
Wasu ma’aikatun gwamnati a yankin dinjiang na yammacin kasar China sun hana al’ummar Musulmi yankin yin azumi a wannan watan na Ramadan.
Wadanda aka hana su yin azumin galibinsu malaman makaranta ne da dalibai da kuma ma’aikatan gwamnati wadanda ’yan kabilar Uighur ne marasa rinjaye.
Wata kungiyar ’yan kabilar ta Uighur ta ce wasu ma’aikartun suna ba da abincin rana kyauta don hana Musulmin gudanar da azumin.
Galibin ‘yan kabilar Uighur sun ce addinninsu da al’adarsu na fuskatar barazana daga shugabannin kasar China.
Hakan na faruwa yayin da hukumomi ke ci gaba da daukar tsauraran matakan tsaro a wannan yankin mai fama da munanan hare-hare.