Ma’aikatun da suka fi samun kudi a kasafin 2024
A karshe Majalisar Dattawa ta fitar da bayanan kudaden da Tinubu ya ware wa ma’aikatu da sauran bangarori a kasafin shekarar 2024
A karshe Majalisar Dattawa ta fitar da bayanan kudaden da aka ware wa ma’aikatu da sauran bangarori a kasafin shekarar 2024 da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar.
A ranar Laraba Tinubu ya gabatar da kasafin na Naira tiriliyan 27.5, ba tare da bayanin kason da ware wa ma’aikatu da bangarori ba, lamarin da ya sa ’yan Najeriya guna-guni.
Sanatoci sun nuna damuwa kan rashin samun karin bayanin kasafin, inda suka bukaci a dakatar da nazarinsa har sai an kawo bayanan.
Sai dai duk da haka Majalisar Dattawa ta kammala karatu na biyu a kan kasafin, washegari da dare Kwamitin Kasafi ya fitar da bayanin abin da ma’aikatu da bangororin za su samu.
Ga jerin ma’aikatun da suka samu kaso mafi tsoka:
- Ma’aikatar Tsaro: Naira biliyan 308.2
- Ma’aikatar Ayyuka: Naira biliyan 521.3
- Ma’aikatar Kudade: biliyan N519.9
- Ma’aikatar Lafiya: Biliyan N304.4
- Ma’ikatar Ilimi: Biliyan N265.4
- Ma’aikatar Wutar Lantarki: Biliyan N264.2
- Kamfanoin Gwamnati: Biliyan N820.9
- Ausun Manyan Makarantu (TETFund): Biliyan N665
- Ma’aikatar Gidaje: Biliyan N96.9
- Ma’aiatar Ruwa: Biliyan 87.7
- Ma’aikatar ’Yan Sanda: Biliyan N69.
- Majalisar Dokoki: Biliyan 198
- Ma’aikatar Neja Delta: Biliyan 324.8
- Hukumar UBEC: Biliya 251.4
- Hukumar Shari’a: Biliyan 165
- Hukumar Arewa maso Gabas: Biliya 126
- Asusun Kula da Lfiya a matakin farko: Biliyan 125.7.