Ma’aikatun gwamnati sun yi watanda da Naira tiriliyan 1.2 —FRC

Ma’aikatu 122 sun ki sanya kudaden shigar da suka tara a asusun Gwamantin Tarayya

Ma’aikatun gwamnati sun yi watanda da Naira tiriliyan 1.2 —FRC

Ministar Kudi ta Najeriya, Zainab Shamsuna Ahmed

Hukumar Kula da Harkokin Kudin Gwamnatin Tarayya (FRC) ta ce ma’aikatu 122 sun ki sanayan kudaden shiga Naira tiriliyan 1.2 da ake tsammani da gurinsu a asusun kasa.

Mukaddashin Shugaban Hukumar, Barr. Victor Muruako, ya bayyana haka a wajen taron manyan jami’an hukumar, inda ya ce yawanci kudaden da aka ki biya an yi watanda da su ne.

“Bincikenmu ya nuna cewa har yanzu ma’aikatun gwamnati 122 sun gaza biyan gwamnati fiye da naira tiriliyan 1.2, wanda zai iya cike gibin da ake da shi a kasafin kudin bana kamar yadda dokar FRC ta tanadar.

“Mun samu jumlar tiriliyan N1.2 ne bayan an tara adadin kudaden da ake bin ma’aikatun 122 da suka ki biyan kudaden shigarsu. Hakan ke nuni da cewar za a iya gano kudaden, a kuma kwato su”, inji shi

Muruako ya ce, FRC ta tilasta masana’antun gwamnati sun biya Naira tiriliyan 1.7 ta asusun gwamnati, amma an bar hukumar cikin rashin kudi, inda aka ware mata Naira miliyan 380 kacal a kasafin kudin 2020 domin gudanar da ayyukanta.

Da Muruako yake jawabi kan yadda za a shawo kan rashin biyan kudin da ma’aikatun suke yi, cewa ya yi “FRC ba za ta gaji da nanatawa ba cewa, in har gwamnati ta yi amfani da shawarwarin da ta ba ta na tafiyar da masana’antunta kan dokar FRA ta 2007, to gwamnati ba za ta rika bata lokaci wajen karbar bashi daga wasu kasashe ba don gudanar da kasafin kudi.

Ya ce da farko hukumar ta sami ma’aikatu 31 da suka bi doka, sai kuma Ma’aikatar kudi ta karo musu ma’aikatu 92 kamar yadda dokar FRC ta tanadar, wanda hakan ya sa masana’antun suka biya naira tiriliyan 1.7 cikin asusun gwamnati.