Ma’ana da alamomin son Manzon Allah (SAW)
Huduba ta Daya: Dukan godiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya aiko mana Manzo daga mafi tsabtarmu, kuma sanadinsa sai Allah Ya bude idanuwa da zukatan da a da suke rufe, kuma Ya jiyar da kunnuwan da a da kurame ne. Daga nan, wanda duk ke da rabon arziki sai ya yi imani da shi […]
Huduba ta Daya:
Dukan godiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya aiko mana Manzo daga mafi tsabtarmu, kuma sanadinsa sai Allah Ya bude idanuwa da zukatan da a da suke rufe, kuma Ya jiyar da kunnuwan da a da kurame ne. Daga nan, wanda duk ke da rabon arziki sai ya yi imani da shi kuma ya taimaka wa da’awarsa, amma wanda Allah Ya hukunta wa tabewa sai ya karyata kiransa kuma ya kawar da kai daga gare shi.
Bayan haka, ya ’yan uwa masoya Allah da ManzonSa! Hakika rubuce-rubucen masana daga cikin Musulmi da wadanda ba Musulmi ba, sun hadu a kan cewa Annabinmu Muhammmad (SAW) shi ne ya fi amfanar da kowa a duniya, kuma shi ne mafi karimcin mutane, kuma shi ne mafificinsu. Kuma ya fi kowa daraja a wurin Allah. Kai Manzon Allah (SAW) ya fi kowa ilimi, kuma ya fi kowa tsentseni (gudun haram), kuma ya fi kowa gudun duniya. Ya fi kowa adalci, ya fi kowa dauriya (hakuri yau da kullum), kuma ya fi kowa baiwa. Shi ne kan gaba a wajen kunya da tawali’u! Kai, kyawawan halayen Manzon Allah (SAW) ba su kidayuwa!
Da ma Allah Ya ce : “Lallai ne kai (Muhammadu) kana a kan manya-manyan halaye masu girma.” (Alkalam: 4).
Ku tuna ya ’yan uwa irin yabon da masana tarihi daga cikin Turawan Yamma suka yi wa Manzon Allah (SAW). Daga cikin akwai:
Edward Gibbon (1737-1794): A zamaninsa ba masanin tarihi Bature irinsa. Ga abin da yake cewa da Ingilishi:
“The creed of Muhammad is free from the suspicion of ambiguity, and the Kur’an is a glorious testimony to the unity of God.”
Ma’ana: “Babu rudani a cikin akidar Muhammadu, kuma Alkur’ani babbar hujja ce a kan kadaitar Allah.” (Dubi littafinsa “The History of the Decline and Fall of the Roman Empire.” Kamar yadda Ahmad Deedat ya ambata a sannanen littafinsa “Al-Kur’an the Ultimate Miracle.”
Dokta Micheal H.Hart, shi kuma Kirista ne Ba’amurke, a shahararren littafinsa “The 100 Most influencial Men in History,”(Wato mutum 100 da suka fi tasiri a tarihi), inda ya tantace mutanen da suka fi kowa amfanar da dan Adam a duniya, tun daga Annabi Adam (AS); ya tsattsara su gwrgwadon amfanarwarsu. Abin mamaki, sai wannan Kirista ya zabi cewa Annabinmu Muhammad (SAW) shi ne na farkonsu! Wato, a iya nazarinsa da bincikensa da kalelecewarsa, Annabi (SAW) ya fi kowa amfanar da dan Adam! Allahu Akbar! Ga ma dalilinsa na zaben shugabanmu a wannan babban matsayin (a cikin Ingilishi):
“He (Muhammad) was the only man in history who was supremely successful on both religions and secular lebels.”
Ma’ana: “A tarihi, Muhammad ne kawai ya ci gaggarumar nasara a fagagen addini da rayuwar duniya.”
To, wadannan ba su ke nan ba, mun dai ambaci kadan ne saboda karancin lokaci.
Ya jama’a idan muka lura, duk fa wannan yana karfafa yabon da Allah Madukakin Sarki Ya yi ga Annabinmu (SAW) da sahabbansa ( Allah Ya kara musu yarda) a Alkur’ani Mai girma da kuma littattafan da suka gabaci Alkur’anin. Ayoyin da ke dauke da wannan yabon suna da yawa kuma sannanu ne. Bari mu ambaci wannan aya daya ta wadatar da mu saboda ba lokaci:
“Kuma wadanda suka gabata na farko, na daga Muhajirina da Ansaru, da wadanda suka biye musu da kyawawan (ayyuka) Allah Ya yarda da su, kuma sun yarda da Shi, kuma Ya yi musu tattalin gidajen Aljanna wadanda korammu ke gudana a karkashin (benayen)su, suna masu dauwama a cikinsu har abada. Wancan (samun haka) shi ne babban rabo mai girma.(At-Tauba: 100).
Ku ji da kyau ya jama’a! Kamar yadda hatta wadanda ba Musulmi ba suka yabi Manzon Allah (SAW), haka su ma sahabbansa suka samu irin wannan yabo daga ma’abuta ilimi daga gare su. Misali, ku saurari abin da wannan shahararren masanin tarihi (mutumin Lebanon da ya rayu, kuma ya rasu a Masar) wato Jurji Zaidan (1861-1914) yake fada game da Sayyiduna Umarul Faruk, yana mai girmama shi, yana cewa : “Shi ke kasancewa farkon wanda yake aikata abin da yake kira zuwa gare shi.”
Kuma ya ce: “Shi (Umar) mai adalci ne ga dukan mutane, kuma mai halin girma ne (karimci) hatta ga wadanda ba Musulmi ba.”
To, ya ku ’yan uwa! Shin wanda wadancan zababbun mutane suka kasance su ne jagororinsa, me ya rage gare shi illa ya doge da karatun tarihin rayuwarsu da kokarin koyi da su da riko kyam ga tafarkinsu, domin shi ma ya rabauta a duniya da Lahira, kamar yadda su ma suka rabauta.
Ya Allah, Ka sanya mu cikin masu koyi da su, kuma ka tayar da mu tare da su ya Ubangijinmu! kuma Ka sanya mu cikin masu samun babban rabo tare da su, amin.
Huduba ta Biyu:
Ma’ana da kuma alamomin son Manzon Allah (SAW):
Godiya ta tabbata ga Allah Wanda Yake hallita abin da Yake so kuma Yake zabi. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga Annabi zababbe da jama’ar gidansa tsarkaka da sahabansa managarta.
Bayan haka, ya ku bayin Allah! Ba shakka imani da Annabi (SAW) da yi masa biyyaya da koyi da shi da kuma sonsa farilla ne, lazimi, a kan kowane mumini, ba makawa. Allah Madaukaki Ya ce:
“Ka ce in kun kasance kuna son Allah, to, ku bi ni, sai Allah Ya so ku, kuma Ya gafarta muku zunubbanku.” (Ali Imran : 31).
Kuma an ji daga Anas (RA) cewa Manzon Allah (SAW) ya ce: “Imanin dayanku ba ya cika har sai na fi soyuwa a gare shi fiye da dansa da mahaifinsa da mutane baki dayansu.” (Buhari da Muslim suka ruwato).
Ma’anar son Allah da ManzonSa:
Shaharraren malamin nan mai littafin “Asshifa,” wato Alkali Iyal ya fadi cewa, “Abin nufi da cewa bawan Allah yana son Allah da ManzonSa shi ne, biyayyarsa ga Allah da ManzonSa da kuma yarda da abin da suka yi umarni.”
Alamomin son Annabi (SAW):
Har ila yau dai, mai littattafin Asshifa ya kebance wani fasali a cikin nagartaccen littafinsa game da alamomi da dalillan masoyan Manzon Allah (SAW). Bari mu ambaci wasu daga cikinsu, tare da takaitawa:
Koyi da shi: Duk mai son Annabi zai rika yin koyi dashi, (Sallallahu alaihi Wasallam). Kuma zai rika aiki da sunnarsa. Zai rika bin zancensa (SAW) da ayyukansa, tare da bin umarninsa da kuma nisantar hane-hanensa. Zai ladabtu da ladubbansa – ko a cikin sauki ko a cikin tsanani, ko yana so ko baya so.
Yawan son haduwa da Mnzon Allah (SAW): Domin duk masoyi yana son haduwa da masoyinsa.
Yawan ambatonsa (SAW): Tare da girmama shi a wajen ambatonsa da kuma bayyana khushu’i da tawali’u idan mutum ya ji an ambci Manzo (SAW).
Son duk wanda Manzon Allah (SAW) ke so na daga jama’ar gidansa da sahabbansa: Muhajiransu da Ansarunsu da kuma kin duk wanda yake kinsu, ko yake zaginsu. Ba shakka, duk wanda kake so, to kuwa kana son abin da yake so!
Annabi (SAW) ya ce: “Ina tsoratar da ku Allah! Ina tsoratar da ku Allah game da sahabbaina! Kada ku mayar da su maharba (inda ake son harbi ya kai, wato ababen zargi da zagi) a bayana. Duk wanda ya so su to, saboda son da yake yi mini ne yake sonsu. Kuma duk wanda ya ki su, to, saboda kiyayyar da yake yi da ni ne yake kinsu. Duk wanda ya cutar da su, to, ya cutar da ni,duk wanda ya cutar da ni, to, hakika ya cutar da Allah; kuma duk wanda ya cutar da Allah, to Allah Ya yi kusa Ya kama shi.” (Tirmizi ne ya ruwaito).
Tausayin al’ummar Manzon Allah (SAW): Da yi wa al’umma nasiha da fadi-tashi domin maslahohinta da kare al’ummar daga abin da zai cutar da ita, kamar dai yadda shi Manzon Allah (SAW) ya kasance mai tausayi, mai jinkai ga muminai.
Bari mu wadatu da abin da ya saukaka nan ya ’yan uwa, duk da yake ba iyakar bayanin ke nan ba.
Allah Ya yi mana albarka, kuma Ya albarkanci abin da muka ji. Allah Ya sanya mu cikin masoyanSa, kuma masoya ManzonSa a duniya da Lahira. Ya Allah! Ka ba mu abu mai kyau a duniya, Ka ba mu abu mai kyau a Lahira, kuma Ka kare mu daga azabar wuta. Ya Allah! Ka taimake mu a kan makiyanmu.
Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu, Annabi Muhammad (SAW) da jama’ar gidansa da sahabansa baki daya.
Wassalamu alaikum.
Injinya Isma’il M. Cindo Gotomo (MNSE,MNIAE), Limamin Masallacin Juma’a na Haliru Abdu, Birnin Kebbi, za a iya samunsa ta tarho: 08036049452 ko imail: [email protected].