Ma’auni da sikeli na da matuqar amfani ga tattalin arziki – Injiniya Sidi
Injiniya Muhammed Sada Sidi, Shi ne Daraktan Sashen Awon Nauyi da Sikeli wato ‘Weight and Measures’ da ke Ma’aikatar Ciniki da Masana’antu ta Kasa. A tattaunawarsa da Aminiya, Injiniya Sidi ya bayyana alfanun da ke tattare da ma’aunai da sikeli wajen karfafa tattalin arzikin kasa. Inda ya ce sashen zai iya samar da Naira biliyan […]

Injiniya Muhammed Sada Sidi, Shi ne Daraktan Sashen Awon Nauyi da Sikeli wato ‘Weight and Measures’ da ke Ma’aikatar Ciniki da Masana’antu ta Kasa. A tattaunawarsa da Aminiya, Injiniya Sidi ya bayyana alfanun da ke tattare da ma’aunai da sikeli wajen karfafa tattalin arzikin kasa. Inda ya ce sashen zai iya samar da Naira biliyan 20 a duk shekara. Don jin wannan da ma wasu batutuwan, ga yadda hirar ta kasance kamar haka:
| Ranka ya dade ko zaka fara da takaitaccen tarinka saboda makaranta? |
Sunana Muhammed Sada Sidi, an haife ni a Garin Sakkwato a shekarar 1960. Na yi makarantar Furamare ta Gulmawa inda na karasa a Kapital, daga nan na tafi Sakandare ta Gwadabawa a Sakkwato. A 1985 na fara aiki a Mai’aikatar Ayyuka ta Jihar Sakkwato. Daga nan kuma na samu gurbin karatu aka tura ni Kasar Indiya inda na yi karantun Injiniya, bayan na kammala na dawo gida na ci gaba da aikina, sannan a 1998 na samu kaina a wannan ma’aikata ta Ciniki da Masana’antu bayan na samu digiri na biyu a Jami’ar Usman Danfodio da ke Sakkwato. Ina nan har Allah Ya kawo ni wannan matsayi na Darakta a Sashen Awon Nauyi da Sikeli (Weight and Measures) na wannan ma’aikata.
A matsayinka na Daraktan wannan sashe na Awon Nauyi da Sikeli, a karkashin Ma’aikatar Ciniki da Masana’antu. Wane rawa kake shirin takawa don ganin wannan sashe ya bambanta da lokutan baya?
Wato ina da gagarumin aikin da na ke fatan cimma nasara akansa, kuma ina riokon Allah Ya ba ni ikon yi din, domin muhimmancin da wannan sashe ya ke da shi wadda kuma mutane da yawa ba su sani ba. Domin wannan ne sashen da Gwamnatin Tarayya ta kebe wanda zai kula da dukkan ma’aunan da ake amfani da su a sha’anin tattalin arzikin kasa ta fuskar cinikayya a ko’ina cikin fadin kasar nan. Kundin tsarin mulkin kasa ya tsara wannan cewa ita ce za ta kula da dukkan ma’auni, ko na tsaba ko na ruwa ko na awon yadika da sauransu, don tabbatar da cewa babu wanda aka cutar. To wannan shi ne aikinmu. Amma wannan sashen ya samu koma-baya, koda yake na ta’allaka wannan ga rashin fahimtar da shugabannin baya suka yi wa asalin muhimmancin aikin wannan sashe. Idan da sun san muhimmancin sashen, da wani shugaba bai dubi kowane bangare na tattalin arziki fiye da wannan ba!
Saboda babu yadda za a yi wata sana’a ko wani ciniki ya karfafa idan ba a tabbatar da adalci cikin ciniki ba. Wanda kuma shi ne aikin da wannan sashen ya kafu akansa. Na farko abinda na ke son in fara yi shine in watsa manifofin wannan sashe ga al’umman Najeriya, sannan su san ta ina zai shafi rayuwarmu, a matsayinmu na ‘yan kasuwa, a matsayinmu na manoma da kuma a gwamnatance. Domin wasu kasashe sun dauki wannan da muhimmancin gaske kuma suna amfana da shi. Amurka ce kan gaba wajen baiwa wannan sashe muhimmanci ba kamar anan kasashen Afirka ba. To ina da kudurin yada manufar wannan sashe don gwamnati da al’umma su fahimta, don su san ta inda za su bada gudumawa. Ta yadda talaka zai san inda zai kai kokensa idan an zalunce shi wajen ciniki.
Sannan musamman ku ‘yan jarida akwai rawar da za ku taka wajen isar da wannan sako ga al’umma, muddin ba tashi tsaye aka yi ba, to duk kokarin da Gwamnatin Shugaba Buhari ta ke yi wajen janyo hankalin masu zuba jari a Najeriya abin ba zai yi wu ba. Domin sai ka tabbatar da cewa akwai ingantaccen shiri na ciniki a kasarka sannan kake gayyato bako don ya shigo har ya sanya dukiyarsa don ya samu wani abu har ita ma kasa ta samu. A yau idan ka sayi mudun masara anan Abuja, idan ka je Kebbi ka sake auna shi, da wuya ka same su daidai. Babban kokarinmu shi ne mu maida ma’aunanmu bai daya, idan aka cimma wannan buri ‘yan kasuwa suka bada hadin kai kamar yadda hukuma da Allah da KanSa Ya bada umarni akan ma’auni, to nasarar farko kenan, cewa duk abinda zaka saida, ka saida shi bisa sikeli. Yau idan ka je kasuwanninmu, ko tattase da tumatir babu ma’auni haka ake sayarwa mutane, me saye bai san abin da ya saya ba, wanda ya sayar bai san abin da ya saida ba. Sannan abu na biyu da muke fata shi ne gwamnati ta ba mu hadin kai ta yadda zamu kai ma’aikatanmu su karo ilmi a kasashen da suka ci gaba ta wannan fanni, domin babu wata kafa ta ilmi a yau a Najeriya da za ta koyar da kai wannan aiki, saboda babu shi ma cikin tsarinmu na karatu sam, illa kawai anan cikin ma’aiktar ne mu ke bada horo. Sannan da kuma kayan aikin kansu.
Kila wani zai yi mamakin cewa ta ina gwamnati za ta amfana ta fuskar daidaita ma’aunai?
Wato idan aka daidaita ma’aunai, to kudin shiga za su samar, za a samu kudin shiga masu yawa. Domin a takaice wannan sashe zai iya samar wa gwamnati kudin shiga kimanin naira biliyan 20 a duk shekara, wannan ma fa ba ayi maganar baki masu shigowa ba. Ka ga wannan ba karamar gudumawa ba ce ga sha’anin tattalin arzikin kasa. Idan ka inganta harkokin kasuwancinka kasashen waje za su shigo, domin babu mai son ya yi asara, sannan kamfanoninmu za su girma, wadanda suka mutu kuma za su tashi.
Idan muka kom can gida, a makon jiya ne Allah Ya yi wa Uban Doman Sakkwato, Alhaji Sada Sidi Suyudi, wanda ya ke mahaifi gareka. Shin ya za ka kwatanta wannan rashin?
To hakika wannan rashi babba ce, ba wai kawai mu iyalansa ba, rashi ne ga Al’ummar Sakkwato baki daya, musamman idan ka yi la’akari da yadda mutuwar tasa ta girgiza jama’a. Domin har yanzu al’ummar sakkwato na jimamin wannan rashi. Don haka wannan rashi ne da ba zamu taba mantawa da ita ba. Kuma Alhamdulillahi an bizine shi a Hubbare ne ba gidansa ko a makabarta ba.
Wadanne halayya za ka tuna marigayin tsawon tasowarka?
Hakika tun tasowa ta na samu marigayi Uban Doma a matsayin malami, ya yi karantarwa a makarantu daban-daban, kamar su Nizamiya da STC Sokoto, Kuma Marigayi Sardauna da kansa ya ba shi wannan aikin, daga bisani ya tafi SS Kano don neman karin ilmi na zamani baya ga wanda yake da shi na zaure. Don babban abin da na san shi akai shi ne kullum ya na cikin hidimar neman ilmi da kuma bayar da shi. Haka kuma ya dan samu wani lokaci da ya yi aikin shari’a har ya zama Khadi na Jihar Sakoto, daga bisani shi da kansa ya rubuta ya ajiye aikin! A takaice dai rayuwarsa ta kare ne akan sha’anin karatu da karantarwa.
Kasancewarsa babban alkali, akwai wata shari’a da ya taba zartarwa wacce ta baka mamaki ko sha’awa da ba za ka manta ba?
A lokacin da ya yi ayyukan shari’a mu na raya kwarai, ba mu da wayon da zamu tantance halin da ake ciki. Amma dai na san ya rayu ya na ba mu labarin wadansu al’amura da shari’u da ya yi a baya. Akwai wata shari’a da ya taba ba mu labari sannan ya na yawan nanata mana ita bisa yadda yake godiya ga Allah da Ya ba shi ikon yin shari’ar yadda ta ke. Ya taba samun kansa a wani gari da ake kira Kamba a matsayin alkalin garin, ya je a lokacin nan bai da masauki, inda wani attajiri a garin ya ba shi gida ya na zaune da iayalansa tsawon shekaru fiye da biyu cikin wannan gidan. Ana nan wata rana sai shari’a ta kama wannan maigidan da wani talaka akan rigimar filin noma. Shike nan aka tattaro shari’ar nan aka kai gabansa, bayan bincike da dabarun alkalai Uban Doma ya fahimci cewa wannan attajirin da yake zaune a gidansa ne ba shi da gaskiya a shari’ar, wurin nan lallai na talakan ne. To sai kuwa Allah Ya taimake shi ya yanke shari’ar nan yadda ta ke, ya ba talakan gaskiyarsa. Sai ya ce mana daga fitowarsa a kotun sai ya tafi neman wani gida don ya tashi a gidan attajirin, saboda ya na tunanin kila ya kwace gidansa, kuma abin da ya faru kenan. To hakika ya na alfahari da wannan shari’a kwarai.
Ku iyalansa ya ya ku ka ji da wannan karramawa da aka yi ta bizine shi a Hubbare, shin da ma ya bar wasiyyar hakan ne ko kuwa?
Hakika wannan karamcin abin yabawa ne, saboda lokacin da Allah Ya yi ma sa rasuwa sai muka sanar da Mai Alfarma Sarkin Musulmi, domin ya dauke shi uba kuma har gida yake zuwa ya gaishe shi. To mu ka shaida masa sai ya ce maza a shirya shi a kawo shi nan Kofar Sarkin Musulmi ayi masa jana’iza kuma a kai shi Hubbare a rufe! To gaskiya ba mu da wannan tunanin, ba mu taba sanin hakan za ta faru ba. Don haka gaskiya ba mu da kalaman da zamu yi amfani da su wajen godewa Mai Alfarma Sarkin Musulmi bisa wannan alfarma da aka yi wa Uban Doma. Allah Ya jikansa Ya kuma saka da alkhairi.
A matsayinka na daya daga cikin ‘ya’yansa maza. Ko kana da sha’awar ka gaji rawaninsa?
Ni ne ma babban dansa namuji. Kuma tabbas duk wanda ya fito daga waje irin haka, to ya na da muradin ya gaji wurin ko ya gaji halinsa. Sannan kuma da ya ke gida ne babba, domin in ka dauke gidan Sarkin Musulmi babu gidan da ya kai shi yawa saboda iyalai ne kashi-kashi kuma kowa ya na bukata. E lallai ni kaina ina so, amma dai saboda karfafa zumunci tare kuma da kaucewa sabani, mu duka mun taru mun yi ittafakin mu bar wa wani kaninsa ya ci gaba daga inda Uban Doma ya tsaya. To mun yi wannan sai dai kawai aiwatarwa muna shirin zuwa mu sanar da Sarkin Musulmi domin shi bai sani ba yanzu haka.