Ma’aunin hawan Jini
Aminiya samu tattaunawa da Gambo Abdul’aziz, wani fitaccen mai gudanar da gidan wasan gargajiya, inda ake gudanar da wasannin dabe da dambe da kokawa da raye-raye da kade-kade, wanda aka yi masa lakabin Gidan Dirama Na Zinariya, Unguwar Ajah a Legas. Ya bayyana yadda aka yi ya samu nasarar kafa gidan nishadantar da jama’a a […]
Aminiya samu tattaunawa da Gambo Abdul’aziz, wani fitaccen mai gudanar da gidan wasan gargajiya, inda ake gudanar da wasannin dabe da dambe da kokawa da raye-raye da kade-kade, wanda aka yi masa lakabin Gidan Dirama Na Zinariya, Unguwar Ajah a Legas. Ya bayyana yadda aka yi ya samu nasarar kafa gidan nishadantar da jama’a a Legas. Ya yi bayani dalla-dalla dangane da kalubalen da yake fuskanta da sauran batutuwa da yawa.
Za mu so ka gabatar da kanka?
Sunana Gambo Abdul’aziz. Yau shekarata kimanin 38 a duniya. Na yi karatun zamani tun daga makarantar firamare zuwa sakandire a garinmu na Hadeja. Ni ne shugaban gidan dirama da ake kira Zinariya Adbance Shukuran Production da Turanci amma a yaren Hausa ana kiran gidan da suna ‘Gidan Dirama Na Zinariya.’
Me ya sa ka sanya wa gidan sunan Gidan Dirama Na Zinariya?
Abin ya samo asali ne yadda na fara harkar tun a Arewacin Najeriya. Ni dai mutumin garin Hadeja ne kuma na fara wannan harkar tun daga shekaru fiye da 22 da suka wuce. A lokacin da na fara, sunan kungiyata ‘Hadeja Emarate Production.’ A lokacin ina karkashin Sarkin Fulanin Hadeja. Da tafiya ta yi tafiya sai kowa ya kama gabansa daga cikin ’yan wasan, sai na sake mata suna zuwa ‘Haske Production.’ Muna tafiya a haka sai na sake mata suna zuwa ‘Shukura Pruduction.’ Daga bisani bayan abubuwa sun sauya a Arewa, sai na yanke shawarar dawowa jihohin Kudu domin na ci gaba da gudanar da harkokina na nishadantar da jama’a. A yau na shafe shekaru kimanin goma sha daya ina gudanar da wannan harka a Jihar Legas.
Me ya sa ka bar Arewa ka dawo Jihar Legas da ke Kudancin Najeriya?
Gaskiya abin da ya sa na dawo Legas shi ne, a Arewa da aka bullo da shari’a sai ya zamana harkokinmu sun tsaya cik. To ka san ita wannan harka ta zama tamkar jinin jikina. Ita na sani kuma ita ce hanyar neman abincina, da ita nake rayuwa. Saboda haka sai na yi tunanin cewa bari na dawo Kudu na ci gaba da gudanar da harkokina. Sai kawai na taho nan. Ina zuwa sai na sake wa kungiyata suna zuwa ‘Zinariya Adbance Shukara Production’ wanda a Hausance ake kira Gidan Dirama Na Zinariya.
Wadanne irin wasanni kake gudanarwa a wannan gida?
Ina gudanar da wasan rawar koroso da wasannin dabe da gudanar da wakokin zamani na Hausa. Ni kaina ina yin wakokin Hausa. Ina yin dambe da wasan kokawa don nishadantar da jama’a da sa su dariya don su manta bakin ciki da damuwar da take damun su.
Wadannen nasarori za ka iya bayyanawa ka samu tun lokacin da ka fara wannan harka?
Na gode wa Allah don na samu nasarori da yawa sakamakon wannan harka. Na samu abin duniya da hada alaka da mutane. Kuma yanayin wasanni da nake yi a yanzu ya bambanta da yadda nake yin su a da. Don a yanzu wajen gudanar da dirama muna sanya abubuwan zamani kamar harshen Turanci da Yarabanci. Wannan babbar nasara ce a gare ni don ni ba Hausawa kawai suke kallon wasana ba, dukkan kabilu Yarabawa da Kwatakwali da ’yan Ghana da ma wanda Turanci kawai yake ji, idan ya zo gidan diramarmu zai fahimci wasannin da muke yi saboda sanya yarukan da muke yi a ciki.
Wadannen matsaloli za ka iya bayyana ka gamu da su?
Gaskiya na gamu da matsaloli da yawa, musamman kamar ta bangaren gudanar da ayyukanmu. Misali, nan ba yankinmu ba ne da za ka samu wuri na dindindin. A nan Legas ba haka ba ne. Da ka samu matsala da mai fili sai kawai ya tashe ka. Shi ya sa a nan yankin Aja na yi gidan dirama guda shida ke nan. Saboda haka rashin takamaiman wurin zama ko in ce fili na dindindin da za ka bude katafaren gidan dirama ita ce babbar matsalar da take damun mu.
Kana da wasu sababbin wasanni da kake son fara gudanarwa don nishadantar da jama’a?
Akwai wasanni daban-daban. Ina so na kawo wasan Langa. A da a lokacin ina zaune a wata unguwa da ake kira Alaba-Suru ina gudanar da wasan langa saboda haka shi ya sa nake son na kawo shi nan don wasa ne mai mutukar kayatar da jama’a.
Me ye burinka dangane da wannan harka?
Burina shi ne ina so ya kasance duk duniya ta san ni a bangaren bunkasa al’adun gargajiya da nishadantar da jama’a da ilimantar da su da kuma wayar musu da kai. Shi batu na irin wannan harka abu ne mai fadin gaske da ya kunshi abubuwa da yawa. Ban da nishadantarwa akwai ilimantarwa da fadakarwa da kuma nusantarwa.