Ma’aurata 136 sun kashe juna a shekara 4
Wannan al’amari ya rutsa da mata da maza, masu matsayi daban-daban kuma da alamar ya ƙi ci, ya ƙi cinyewa
Alƙaluman da muka tattara daga rahotannin manyan jaridun Najeriya sun nuna yanayin rikicin ma’aurata a ɗauƙacin shiyyoyin shida da ke faɗin Najeriya.
Rahotannin sun nuna matsalolin da suke haifar da hakan a tsakanin ma’aurata da ake zaton zamannsu zai kasance mutu-ka-raba, sun haɗa da zargin cin amanar aure, rikicin abinci, rikici kan waya da sauransu.
Wannan al’amari ya rutsa da mata da maza, masu matsayi daban-daban daga shekarar 2021 zuwa 2025, kuma da alamar ya ƙi ci, ya ƙi cinyewa.
- Ta’addanci: An fi kashe Musulmi a kan Kiristoci a Najeriya — Jakadan Amurka
- Dantawaye ya zama sabon kwamishinan ’yan sandan Abuja
Alƙaluman sun nuna matan aure ne waɗanda suka fi rasa rayukansu a irin wannan yanayi, inda aka kashe mata 96 cikin 136, wanda kusan ninki ukun adadin mazaje 39 da aka kashe.
Akwai kuma wasu miji da mata da suka yi mutuwar, dai wata amaryar da aka kashe ana daf da ɗaurin aurenta.
Ina matsalar ta fi muni?
Bayanan da muka tattara n ma’aurata 134 da aka kashe a Najeriya daga 2011 zuwa 2015 sun nuna matsalar ta fi muni a Jihar Legas, inda aka kashe mutum 17, dukkansu mata in bada mutum ɗaya, wanda ke nuna yadda abin ya fi ritsawa da mata.
A matsayi na biyu wajen munin matsalar akwai jihohi uku — Adamawa da Edo da Ogu — waɗanda a kowannenau aka kashe mutane 10.
Da haka Jihar Adamawa ta zama inda matsalar ta fi muni a yankin Arewa maso Gabas da ma ɗauƙacin Arewa, kamar yadda Legas — wadda Ogun ke bi mata — ta yi fintinkau a Kudu maso Yamma, ɗauƙacin Shiyyar Kudu da ma faɗin Najeriya.
Musabbabin kisan ma’aurata
Masu ɗaukar hankali daga cikin abubuwan da suka faru a Legas sun haɗa da yadda wani magidanci ya cinna wa matarsa wuta, da wani wanda ya kashe matarsa saboda ta ƙi yin girki, sai ta ukun da aka kashe kan ƙin biyan bashi. Akwai kuma wadda mijinta ya cizge iskar Oksijin da take shaƙar numfashi da shi a gadon asibiti.
Waɗannan abubuwan sun nuna yanayin raunin alaƙa tsakanin ma’aurata inda wani lokaci abin da bai kai ya kawo ba yake rikiɗewa zuwa tashin hankali a tsakaninsu.
A Jihar Edo, inda abin ya fi muna Kudu maso Kudu, dalilan wannan ɗanyen aiki sun haɗa da tashin hankali, rashin kwanciyar aure da rikicin kuɗi — wani abin mamaki shi ne yadda wani ya kashe matarsa saboda “ta ƙi ranta mishi N2,000.”
A Jihar Ogun, inda nan ma aka kashe mutum 10, dalilan sun haɗa da cin amanar aure da kuma rikici kan dukiyar iyali.
Sauran jihohi da aka fi samun matsalar su haɗa da Anambra (9 cases), Delta (7) da Ondo (7) — dukkanau a Shiyyar Kudu, a birane da ya yankunan karkara.
Ra’ayin Malami
Rabaran Amos (ba sunansa na gaske ba) daga Cocin Anglican St Matthias, Ushafa, ya bayyana cewa waɗannan kashe-kashen ba kwatsam suka faru ba haka kawai, illa sakamakon lalacewar dangantaka na tsawon lokaci.
“Kisan ma’aurata ba ya faruwa da gaggawa. A cikin kowanne tashin hankali akwai tarihin bacin rai, riƙo, girman kai da watsi,” in ji shi.
Ya ce rashin iya magana da fahimta na daga cikin manyan dalilan rikici. Ma’aurata da dama ba sa tattaunawa don fahimtar juna, sai don yin rinjaye.
Rabaran Amos ya danganta matsin tattalin arziki da ƙaruwar rikici a gidajen aure. Ya ce Rashin aiki da tsadar rayuwa na rage haƙuri da kwanciyar hankali.
“Talauci ba ya haddasa kisa kai tsaye, amma yana ƙara tsanani ga duk wata matsala.”
Ya ce rashin amana da zargin zina na rushe dangantaka, inda gida ke iya biyowa baya. Kishi, fushi da giya na haddasa kisa.
Ya ƙara da cewa wasu maza na ɗaukar dukan mata a matsayin alamar iko.
“Wasu maza na ganin cewa duka alamar shugabanci ne; wasu mata kuma na mayar da martani da ƙin yarda. Idan ƙauna ta koma gasa, an manta da manufar aure — zama tare da fahimta.”
Ya ja hankalin ma’aurata da su nemi taimako da wuri: “Shiru a yanayin tashin hankali ba tsoron Allah ba ne. Duk wani kisa yana farawa da sakana zuciya. Idan ba a tumɓuke ta ba, sai ta girma ta zama masifa. Dole ne mu gina gida da yafiya, haƙuri, addu’a da girmama juna.”