Ma’aurata a daina cin zarafin juna
Za mu so mu kawar da kai game da yadda ake take hakkokin mata a gidaje, duk yadda abin ya zama jiki ga ma’aurata. Idan da ana daukar mataki kan yadda ake cin zarafin mata a Arewacin kasar nan, za a taimaki al’umma, kuma za a bunkasa tattalin arziki, domin wannan dabi’a ta fi yawa […]
Za mu so mu kawar da kai game da yadda ake take hakkokin mata a gidaje, duk yadda abin ya zama jiki ga ma’aurata. Idan da ana daukar mataki kan yadda ake cin zarafin mata a Arewacin kasar nan, za a taimaki al’umma, kuma za a bunkasa tattalin arziki, domin wannan dabi’a ta fi yawa a Arewa, shi ya sa a Kano ana maganar zaurawa dubbai ba daruruwa ba. Akwai dalilai da dama da suke sa ake cin zarafin mata a sassa daban-daban na kasar nan koma a duniya baki daya, duk da babu wata kididiga da za ta nuna tsakanin mata da maza wa aka fi cuta.
Cin zarafin mata na da sigogi, ya kan zo da sigar takurawa, take hakki hakan kan kai ga fyade. A wa yara fyade, wani ma matarsa yake wa fyade, haka yadda luwadi da madigo suka zama ruwan dare don a wajen wasu sauki ne, maimakon a kashe kudi wajen sayen kayan lefe, da dadin baki ma sai a biya bukata! Yayin da wannan fitinar na karuwa a dalilin tabarbarewar tattalin arziki, wanda kan haifar da rashin hakuri da hauka a wani yanayin.
Bincike ya tabbatar da cewa kowa zai iya zama sabon salon zaluntar dan uwansa tsakanin ma’aurata, ta bangaren duka mata sun fi shan wuya, kusan da wuya mace ta daga hannu ta doki miji, sai dai muskilanci irin na ‘ya mace.
A halin yanzu wasu mata sun bazama suna kamfen kan a haramta auren wuri, amma ba su ce komai ba game da zinar wuri ko cudanya tsakanin mata da maza baki, su dai kar yarinya ta auri wanda shekarunsa suka kai na mahaifinta ko kakanta, to idan ita take son mutumin da aure sai yaya?
Ai akwai wadda ke son mai mata, akwai mai amincewa da mai mata uku ya aure ta, ta zama ta hudu! Ko so ku ke mu koma rayuwar Yahudawa, inda miji da mata daya amma a waje kamar bunsuru, duk wadda ya kama sai ya buge, ko kuma so suke a koma rayuwar manyan mata masu kwaikwayon karuwai, kun kama gida ku kadai ba aure, kun ki komawa tsohon gidanku, kun ki sabon aure, kun tara ‘yan mata, kune kawalci, kune a tarrurukan siyasa.
Za a iya cewa tattalin arziki kan taka rawar gani wajen matsalolin cikin gida da suka hada da cin zarafi, duka ko ma saki, wani lokaci saurin fushi da zafin nama kan jawo a yi mari ko bada takarda, shi yasa sau da yawa abin da bai kai ya kawo ba kan sa a sami sabanin da yake ba kowa mamaki. Wadanda suka yi aure don soyaya, kafin a je ko’ina sai a rabu, wata daga nan an bata rayuwarta, musamman wadda bata yi karatu ba.
Samar wa mata ayyukan yi kadai zai kawo saukin wannan dabi’a, yayin da maza da dama na bakin ciki matansu su yi karatu ko aiki a bisa wasu ra’ayoyin da suka ci karo da addini. Har yanzu mutane kan ba al’adu muhimmanci fiye da addini. Abin bakin cikin shi ne kai maigida ka bar al’adun ka zama dan birni ka hanawa matarka, mahaifiyar ‘ya’yanka ‘yancin da addini ya bata na neman ilimi ko aiki don tallafawa gida.
Sau da yawa maza kan kara aure saboda matan ba su iya biyan bukatar mazan, domin matan ba su da tsafta, ba su san abincin da za su ci ni’imarsu ta karu ba, sai bin malamai, bokaye da gulma. Masu dan karatu kuma sai girman kai da rashin iya bakinsu, inda mace za ta rika tona asirin mijinta a wurin iyaye, kawaye ko kafofin yada labarai!
Wani ba ya da hakuri, da abubuwa sun cushe masa, sai ya dauki matakin da bai yi niyya ba. Wadannan ba abubuwan kau da kai ba ne, idan yarinya ta yi aure, duk matsalolinta ta warwaresu tsakaninta da mijinta, ba wanda ya kai su kusanci, aljannar ta a hannun shi, fatan kowa cikinsu rai ya raba. Ba wanda yake daukar laifin wani, mu gyara zukatanmu.
Wajen kawo karshen cin zarafin mata, ana bukatar al’umma, musamman iyaye ko wakilai su sa-ido tun a tashin farko a san wane ne za a ba yarinyar, ki san wa za ki kawo gida. A sa yara a turbar girmama na gaba, su san miji aboki ne, kuma uba ne, shi ne a sama! Akwai lada idan mutum ya biya sadakin dan uwansa, ko ya sayo kayan lefe kai kowace gudummuwa ka ba da wajen daurin aure da dauwamar aure, kamar raya al’umma ne.
Ya wajaba miji ya nuna wa matarsa kauna da kauda kai ga kananan abubuwa. Kar ta dame miji da yawan bukatu, musamman kudi, abin da ya ke da muhimmanci shi ne kowa ya san ya kamata, idan ya ce bari, ki bari, idan ya ce yi kaza, ki yi, shi ke nan, ki san yadda za ki yi masa magana, kai kuma ka san yadda zaka tallabota da bata saiti.
Matsaloli tsakanin ma’aurata suna kaiwa ga kunnunwan hukuma ta hannun kotu, a haka alkalai da ma’aikatun da abin ya shafa suke kokarin daidaita lamarin. A nan kowa ya san ya kamata, miji ya mayar da kansa uba, ya san nauyin da ya rataya a wuyansa. Inda muka dauki al’adu da yadda iyaye da kakanni suka rayu a kauyuka zamu ga gargajiyar tafi wajen ma’amala da sanin ya kamata ta yadda ake hada kai a tattauna sabanin yau yadda ake wulakanci da fama da kadaici da talauci.
Su kansu malaman addini suna da rawar takawa a nan, wajen yin huduba kan cin zarafin mata, duka, saki da soyayya. A nan ne wani bagidaje zai fahimci muhimmancin wasa da dariya tsakanin miji da mata da ‘ya’ya. Ba a gwada karfi wajen gwabje mata, kuma da dare ka zo ka same ta! Ragon maza shi ke dukan mata.
Dadin dadawa idan da ana hukunta maza masu fyade, dukkan mata, ko masu saurin saki wadanda da zaran mace ta yi ciki sai su sake ta, ta haihu a gida a kotu ko ma’aikatun da suka dace da taimakon malamai, alakalai da sarakuna da an rage wannan muguwar dabi’ar. Maza su san lokacin aure, kuma mata nawa ya kamata su aura, tare da ba wasu mazan shawarwarin su kara aure, domin wani zai iya rike mata goma sai ka ganshi da daya! Wani ya isa auren amma sai ya ce sai ya gama karatu ko sai ya gina gida! Mawadata su rika tallafawa ma’aurata ko masu niyyar aure don kauce wa zina da sauran fitinun da suka shafi al’umma.
Idan aka wadata maza da aiyyukan yi da sana’o’in hannu, hakan zai bada damar a dauki nauyin dawaniyar da ta danganci iyali. Kuma tun ran farko a gargadi ma’aurata idan mace ta yi laifi a kawo kuka ga mahaifinta kafin a yanke kowane irin hukunci. Amma idan aka bar mutum da yara da mata ba aikin yi, wani ma haushin halin da yake cikin zai iya sawa ya mangare matar ko ya yi kwallo da ‘ya’yan ma bai sani ba!
Abin lura, sau da yawa matan da kan fake da kare hakkokin mata wajen tsawata wa mazaje da hana yara aure, sai ka iske jagororin harkokin kan zama zaurawa, su ki aure, sai zaman zawarci, inda suke neman kudi da wannan harkar, kuma ba sa taimakon mata ko talakawa, kusan ba abin da suke yi da gudumuwar da suke samu daga gwamnoni da attajirai sai kara kayan kwalliya da sayen kadarori.
Wani hanzari shi ne na amfani da kafofin yada labarai wanda ya hada da wasan kwaikwayo, musamman a bisa shirin kungiyoyin kare hakkokin mata da kare rajin bil-Adama su fadakar da mutane game da yadda zaman aure zai yi armashi, muhimmancin biyayya da sharrin zaluntar mata ko miji. A fito da hanyar da mata za su iya kai kukansu ga alkalai ko makusanta don sasanci da kara dankon soyaya tsakanin ma’aurata, ta yadda za a shawo kan muzguna wa juna a boye. Tabbas ba za a samu zaman lafiya a kasar nan ba, sai an saui zaman lafiya a cikin gidaje.
A karshe maza su san an hallice su da zama jagororin al’umma, a hadu don a rufa wa juna asiri, ka rike matarka da kyau, sai a kula da diyarka, kanwarka ta hanyar dauwama a gidan miji. Fatana idan an yi aure rai ya raba.
Buhari Daure [email protected] Modoji, Katsina.