Ma’aurata: Abubuwan Gabatarwa cikin Ramadan (2)

Bude hanyoyin sadarwa tsakanin juna; domin sadarwa ita ke raya zumunta kuma zumunci na tsakanin miji da mata yana da matukar muhimmanci a rayuwarsu da addininsu Assalamu Alaikum, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani kan […]

Ma’aurata: Abubuwan Gabatarwa cikin Ramadan (2)
Ma’aurata: Abubuwan Gabatarwa cikin Ramadan (2)

Bude hanyoyin sadarwa tsakanin juna; domin sadarwa ita ke raya zumunta kuma zumunci na tsakanin miji da mata yana da matukar muhimmanci a rayuwarsu da addininsu

Assalamu Alaikum, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani kan kyawawan ayyukan da ya kamata ma’aurata su dage gabatarwa don inganta so, kauna da zamantakewar aurensu cikin wannan wata mai albarka na Ramadan, da fatan Allah Ya sa mu dace da dukkanin alheran da ke cikin wannan wata, amin.
5. Kyauta da kyautatawa ga miskinai da makwabta:
Sai ma’aurata su yi koyi da Manzon Allah (saw), yadda yake kara yawan kyauta a cikin wannan wata mai alfarma; za su iya yin haka ta wadannan hanyoyin:
• Hada kayan buda baki na alfarma da aikar da su ga marasa galihun da aka san ba su da halin irinsa.
• Gayyatar marasa galihu zuwa walimar buda baki.
• Kyautar kayan Sallah ga mabukata daga ’yan uwa, makwabta da sauran miskinai da sauran makamantan kyawawan ayyuka.
•Tsiro da wani kyakykyawan aiki da kuma dagewa ga aikata shi har sai ya zama dabi’a, kamar yawan murmushi, yawan sada zumunci; saukaka mu’amala ga jama’a; yawan sadaka da taimakon marasa galihu; kyautata zato ga jama’a, yawan yin addu’a ga ’yan uwa Musulmi; dagewa wajen neman ilmi, musamman na kadaita Allah wajen bauta da kuma na yin bautar, yin Salatul Duha; yin Salatul Tauba domin tuba ga Allah daga wani sabo da aka aikata, kuma daga baya aka yi nadamarsa, da sauransu.
6. Ayyukan kara Dankon kauna:
• Ina ma’auratan da ke son kara dadin soyayya da zamantakewarsu, da kara zakaka su da yawaita su? Ga sirri mai kaifin gaske daga Alkur’ani mai girma, shi ne ta hanyar yawaita yabo da godiya ga Allah Madaukakin Sarki. Ma’aurata su tuna dimbin ni’imomi da rahamomin da Allah Ya azurta su da su, su yi ta nanata godiyarsu a kan wadannan ni’imomi kodayaushe, ba dare ba rana. Alkawari ne na Allah, cewa duk wanda ya gode masa a kan wata ni’ima da Ya yi masa, to shi kuma zai kara masa, zai nunnunka masa a kan wannan ni’imar, kamar yadda ya zo a cikin Alkur’ani mai girma:
 “…Lalle ne idan kuka gode, hakika ina kara maku…” (Suratu Ibrahim; Aya ta 7)
Don haka in kuna son karin jin dadin zamantakewarku, sai ku nace gode wa Allah Mabuwayi a kan dadin da kuka riga kuka dandana komin kankantarsa. Kuna son karuwar arziki da wadata? Ku gode Allah a kan wanda ya riga ya ba ku komin kadan dinsa. Kuna son karuwar zuriyya dayyiba da karin kwanciyar hankali? Sai ku gode wa Allah a kan wanda ya ba ku. Kuna iya gode wa Allah koda a kan ni’imar da bai ba ku ba ne da nufin rokon Allah Ya ba ku ita. Don haka a cikin wannan wata na ibada, na amsar addu’a da nunnunkawar ladakun ayyuka, ma’aurata ku dage da addu’ar biyan bukatunku na alheri ta hanyar yawaita yabo da godiya ga Allah Madaukakin Sarki, da kuma neman gafararSa Mabuwayi Mai Hikima.
• Bude hanyoyin sadarwa tsakanin juna; domin sadarwa ita ke raya zumunta kuma zumunci na tsakanin miji da mata yana da matukar muhimmanci a rayuwarsu da addininsu; don haka sai ma’aurata su bude hanyar sadarwa da ke tsakaninsu sosai ta hanyar yawan zama suna tattauna abubuwan cikin rayuwarsu, matsalolinsu da hanyoyin magance su; sannan su watsar da suk wani abu da ke kawo cikas ga dorewar sadarwa a tsakaninsu. In ma wani laifi ne, sai a yafe ma juna kuma a mance da shi take yanke. Kuma ma’aurata su zauna su rubuta burin da suke so su cin mawa a cikin dangantakarsu, kuma su yi ta kokarin aiwatar da shi a cikin wannan wata da kuma bayansa.
• Yin ayyukan ibada tare, da yin ayyukan gida, musamman na hada abincin buda baki tare, duk abubuwa ne da za su kara dankon so da kauna tsakanin ma’aurata.
• Yin buda baki waje daya, maigida ya hada iyalinsa duka, a zauna a ci abinci cikin kwano daya. Yin haka zai matukar kara dankon zumunci da kaunatayya cikin iyali duka.
Abubuwan kara Dankon Soyayya
• Zuwa Sallar Tarawi tare, kuna karatun Alkur’ani, saurarensa ko yin wani zikri kamar addu’ar da ake karantawa in an kama hanyar zuwa masallaci.
• Bayan kammala gabatar da Sallah, maigida maimakon ya yi tasbihi da yatsunsa, sai ya zo ya kama yatsun uwargidansa ya yi tasbihin da su, haka uwargida ma na iya yin haka.
• Maigida ya riki al’adar kullum ya rika rungumar uwargidansa kafin ya fita zuwa wajen aiki. Uwargida kuma ta riki al’adar tarbar maigida da murmushi da shiga mai kyau, tare da ’yar karamar sumba koda ta saman goshi ne ko a kumatu.
• Ma’aurata su samu wani lokaci na musamman su ci abinci tare komin kankantarsa, cikin kwano daya, suna masu ciyar da junansu, kuma suna masu kallon kwayar idon junansu cikin kauna da bege, wannan zai kwararar da soyayyar juna cikin zuciya.
• A dage da karin kyautata wa juna, karin hakuri da juna da karin taimaka wa juna cikin wannan wata, wannan zai kara dankon soyayyar da ke tsakanin ma’aurata.
Sai mako na gaba in sha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koda yaushe, amin.